
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙaramin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya shirya zaman addu’o’i na musamman domin neman nasarar Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027 da ke tafe da zaman lafiya da kuma ci-gaban ƙasa.
An gudanar da taron addu’o’in ne a babban Masallacin Maradun da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara, wanda ya haɗa sarakunan gargajiya, malamai da dubban al’ummar Musulmi.
A yayin jagorantar addu’ar, Sarkin Maradun, Muhammad Garba Tambari ya ce addu’a wajibi ce ga shugabanni da ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada cewa babu wani alheri da ke tabbata ba tare da taimakon Allah ba a kowane mataki.
Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba da Allah ya hore wa Nijeriya a wannan lokaci, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su mara masa baya tare da yi masa addu’ar samun nasara wajen cika alƙawuran da ya ɗauka.
A nasa jawabin, Matawalle ya ce yana da yaƙinin cewa Allah ne ya ƙaddara Tinubu zama shugaban ƙasa domin sake gina Nijeriya da kuma kawo sauye-sauye masu amfani ga al’umma.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa, tare da neman kariya daga duk wata makarkashiya da ka iya kawo cikas ga ci gaban Najeriya.
Matawallen ya ƙara da cewa, addu’a na da muhimmiyar rawa wajen samun nasara, yana mai ƙarfafa al’umma su riƙa komawa ga Allah a dukkan al’amuransu.
Malaman da suka jagoranci zaman addu’ar sun roƙi Allah Ya ba shugabannin ƙasa hikima da basira wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da zaman lafiya da ci-gaba a Nijeriya domin amfanin ‘yan ƙasa a sassa daban-daban.
