Daga AISHA ASAS
A lokuta da dama idan aka ambaci kalmar kwalliya, abin da ke fara zuwa zuciyar mutane shi ne fuska, gashi, tufafi ko kayan shafe-shafe. Wasu kan ɗauki awanni suna kula da waɗannan ɓangarori na jiki tare da kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tabbatar da cewa komai ya kasance cikin tsari da kyau. Amma duk da haka, akwai wani ɓangare na jiki da masana lafiya suka ce ana yi wa riƙon sakainar kashi duk da irin muhimmancin da yake da shi wajen lafiyar mutum baki ɗaya, wato kafa.
Masana likitanci sun bayyana cewa ƙafa ba kawai wani sashe ne na jiki da ake taka ƙasa da shi ba. Ita ce ginshiƙin motsi, tafiya da daidaiton rayuwar ɗan adam. Ita ce ke ɗaukar nauyin jiki tun daga lokacin da mutum ya tashi daga barci har zuwa lokacin da zai koma ya kwanta. Amma duk da wannan muhimmanci, mutane da yawa ba sa ba ta kulawar da ta dace sai bayan wata matsala ta bayyana.
Manyan likitocin fata da na kasusuwa sun ce sakaci da kula da ƙafa na iya janyo matsaloli masu yawa da suka haɗa da warin kafa, fungus, fashewar diddige, ciwon tafin ƙafa, kumburi, lalacewar jijiyoyi da ma wasu cututtuka masu tsanani musamman ga masu fama da ciwon sukari.
Wani babban likitan fata a wani asibitin koyarwa ya bayyana cewa: “Mutane da yawa suna kallon kula da ƙafa a matsayin abin kwalliya kawai, alhali a ɓangaren likitanci ana kallon ta a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin kare lafiyar jiki baki ɗaya.”
ƙafa: ɓangaren jiki mai wahalar aiki:
Masana orthopedic wato kwararrun likitocin ƙasusuwa sun bayyana cewa, kafar mutum tana daga cikin sassan jiki mafi wahalar aiki. Sun ce a cikin ƙafa kadai akwai ƙasusuwa guda ashirin da shida, jijiyoyi da tsokoki masu yawa da ke aiki tare domin bai wa mutum damar tafiya cikin daidaito.
A cewarsu, matsin da ƙafa ke ɗauka a kullum ya fi yadda mutane da dama ke zato. Sun ce mutum kan yi dubban taku a rana ba tare da ya lura da irin wahalar da ƙafafuwansa ke sha ba.
Likitan ƙasusuwa Dakta Sani Musa ya bayyana cewa, mafi yawan matsalolin da ake samu a kafa na faruwa ne saboda rashin kulawa da kuma amfani da takalma marasa kyau.
A cewarsa, “Wasu mutane kan yi shekaru suna sanya takalma masu matuƙar matse ƙafa ko kuma waɗanda ba sa bai wa tafin ƙafa kariya. Wannan kan jawo sauyin tsarin tafiya da ciwon baya da gwiwa daga baya.”
