Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a ranar Litinin ya ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa kan samar da abinci, inda ya buƙaci faɗaɗa ayyukan ban ruwa da gudanar da albarkatun ruwa a faɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake buɗe taron shiyyar Afirka kan noman rani da albarkatun ruwa karo na 6 a Abuja.
Shugaban ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume.
Ya buƙaci ƙasashen Afirka da su yi amfani da sabbin dabaru wajen tunkarar ƙalubalen noman rani da kula da ruwa na nahiyar.
Ya bayyana taken taron, “Ci gaban Noma da Magance Rikicin Ruwa a Afirka,” a matsayin kira na neman matakai don ɗorewar aikin noma da kuma ƙarfin tattalin arziki.
“Afrika na ci gaba da fuskantar manyan aalubale wajen buɗe hanyoyin noman rani saboda rashin isassun ababen more rayuwa, ƙarancin kuɗi, sauyin yanayi, da kuma batutuwan shugabanci.
“Wannan taron ya ba mu wani muhimmin dandali domin mu haɗa kai don tsara hanyar ci gaba,” inji Tinubu.
Ya ci gaba da cewa, ƙasar na da fiye da hekta miliyan 3.1 na ban ruwa da ke kusa da manyan koguna irin su Neja da Benuwai.
A nasa jawabin, ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utseɓ, ya ce gwamnati ta kammala ayyuka da dama a ƙarƙashin shirin ‘Transforming Irrigation Management in Nigeria’ (TRIMING).
Ya sanar da cewa, shirin mai ɗorewa na wutar lantarki da ban ruwa ga Nijeriya (SPIN), zai magance manyan giɓi tare da inganta darajar tattalin arzikin albarkatun ruwa don tallafawa samar da abinci.
“Yayin da aikin TRIMING ya ragu, Nijeriya na shirin fara aiwatar da aikin SPIN tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya,” inji Utsev.
