
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar kai, Alhaji Mohammed Idris ya gargaɗi mutanen da ke ajiye ababen fashewa a gidajensu domin yin ayyukan haƙar ma’adanai ta haramtattun hanyoyi.
A wata sanarwa da Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar, Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a yankin Sabon Pegi na Jihar Neja a lokacin ya je gaisuwar ta’aziyyar waɗanda suka rasa rayukansu a yayin fashewar wani abin fashewa a ranar Litinin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da dameji ga wasu ababe.
Ministan ya ce ajiye ababen fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba yana da haɗari ga rayuka da dukiyoyin masu aikata irin haka, ya na mai kira a gare su da su gaggauta guje wa hakan.
Ya kuma ce tuni Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Ci-gaban Albarkatun ƙasa da Hukumar Wayar da kan al’umma da su sake shirya ɓangaren tare da dakatar da ire-iren ayyukan ta hanyar wayar da kan al’umma game da haɗarin da ke ciki.
Kazalika, Ministan ya ce Shugaba Bola Tinubu na takaicin yadda iftila’i ke haddasa mace-macen al’umma wanda ke ƙara yawaita, inda ya umarci Hukumar Wayar kan al’umma ta faɗaɗa ayyukanta na wayar da kan jama’a don ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.
Haka kuma, ya yaba wa Gwamnatin Neja bisa ƙoƙarinta ga abin alhinin, ya na mai cewa tuni Shugaba Tinubu ya a umarci Ma’aikatar Jin-ƙai da Hukumar bada Agajin Gaggawa da su taimaka ta hanyar bada kayayyakin rage raɗaɗi ga mutanen da iftila’in Sabon Pegi ya afka wa.
