EU ga ECOWAS: Ku nemo sabbin hanyoyin zama tare da Burkina Faso, Mali da Nijar

Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Najeriya da ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka, Ambasada Gautier Mignot, ya yi kira ga ƙungiyar ECOWAS da ta ɗauki wani sabon salo wajen mu’amala da Burkina Faso, Mali, da Nijar bakiɗaya.

Da yake jawabi a Abuja yayin wani taron manema labarai a ranarTalata, Mignot ya bayyana nadama kan ficewar ƙasashen uku daga ƙungiyar ECOWAS, yana mai jaddada cewa haɗewar yankin na da matuƙar muhimmanci wajen samun wadata da kwanciyar hankali.

“Wannan shawara ce da muka yi domin muna matuƙar goyon bayan haɗewar kasashen Afirka ta Yamma. Rabewar bai yi mana kyau ba,” inji shi.

Wakilin, wanda kuma ya zama shugaban wakilai na ECOWAS, ya bayyana mahimmancin tattaunawa da wajen tafiyar da irin waɗannan.

“Ko da kun bar tsarin haɗin kai na yanki, a yanayin ƙasa kun kasance maƙwabta. Dole ne ku nemo sabbin hanyoyin zama tare da haɗin gwiwa,” inji shi, yana mai bayyana goyon bayan EU don taimakawa ECOWAS wajen tafiyar da sauyin.

Yayin da yake kira ga ECOWAS da ta ci gaba da tattaunawa, Mignot ya bayyana cewa, EU za ta ci gaba da yin cudanya da ƙasashen AES, ta hanyar kula da ayyukan jin kai, da daidaita hadin gwiwar raya ƙasa, don mai da hankali kan tallafawa al’ummomin yankin, a yayin da ake fama da matsalar tsaro da yunwa a yankin Sahel.

Mignot, wanda kwanan nan ya karɓi mukaminsa na jakadan EU a Najeriya, ya bayyana ra’ayinsa na inganta hulɗar EU da Najeriya a yayin taron manema labarai.

Da yake bayyana Najeriya a matsayin “babbar jigo a Afirka da ma duniya bakiɗaya,” ya jaddada kudirin ƙungiyar EU na zama amintacciyar aminiyar ƙasar.

Abubuwan da ya sa a gaba sun haɗa da inganta dangantakar tattalin arziki da aka tsara, inganta kasuwanci da zuba jari, da mai da hankali kan sassa tattalin arzikin, fasahar dijital, noma da kiwon lafiya.

A halin da ake ciki kuma, ficewar Mali, Nijar da Burkina Faso daga ƙungiyar ECOWAS, za ta fara aiki ne a ranar Laraba bayan shafe shekara guda ana takun saƙar siyasa, lamarin da ya wargaza yankin tare da barin ƙungiyar cikin makoma mara tabbas.

A ranar 29 ga Janairu, 2024, ƙasashe uku da gwamnatocin sojoji suka jagoranta sun sanar da ECOWAS a hukumance buƙatarsu ta janyewar cikin gaggawa. Amma nassosin ƙungiyar Afirka ta Yamma sun bukaci sanarwar shekara guda don ta yi tasiri.

Hakan dai zai faru ne a ranar Laraba, dukkan ƙasashen ukun sun yi kunnen uwar shegu da kiran da ƙungiyar ECOWAS ta yi na tsawaita wa’adin da watanni shida domin a samu bakin zaren warware rikicin.

ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar a yanzu sun haɗe a wata ƙungiya mai suna ƙawancen ƙasashen Sahel (AES).

Shugabannin nasu na soja na zargin ECOWAS da kakaɓa musu takunkumi na rashin mutuntaka, ba bisa ƙa’ida ba, da kuma haramta juyin mulkin da ya kai su karagar mulki.