Trump ya dakatar da dala miliyan 50 da gwamnatin Biden ta ware don raba ‘kwaroron roba a Gaza’

Gwamnatin Trump ta sanya takunkumi kan tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa, ciki har da dala miliyan 50 da aka ware tun farko don raba kwaroron roba a Gaza.

Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karoline Leaɓitt, ta ce an gano kashe kudaden ne a makon farko na Trump ciki har da sabuwar Ma’aikatar Gwamnatin da ke ƙarƙashin jagorancin hamshaƙin attajirin nan na fasaha Elon Musk.

Yunƙurin Musk da ofishin kasafin kuɗi sun gano cewa akwai kusan dala miliyan 50 masu biyan haraji da suka fita don ba da tallafin kwaroron roba a Gaza,” Leavitt ta faɗa wa taron manema labarai.

Duk da ba ta bayar da ƙarin bayani ba kuma ba a kai ga tabbatar da asusun ba kai tsaye ba.

Kwaroron roba gabaɗaya farashin ƙasa da dala ɗaya kowanne a Amurka kuma ƙasa da yawa. Sama da mutane miliyan biyu ne ke rayuwa a Gaza, duk da cewa, kaso mai nauyi na mutanen sun mutu a tsakanin watanni 15 da yaƙi ya ɓarke tsakanin su da Isra’ila

Leavitt ta kuma ce Amurka na shirin bayar da dala miliyan 37 ga Hukumar Lafiya ta Duniya kafin Trump ya sanar da ficewa daga ƙungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya.

A take bayan hawansa mulki, Trump ya ba da umarnin dakatar da tallafin na ƙasashen waje na tsawon kwanaki 90.

Ya sha alwashin sake dubawa don tabbatar da cewa taimakon ya dace da manufofin gwamnatinsa, wanda ke adawa da zubar da ciki, yancin ɗan adam da shirye-shiryen sauyin yanayi.

Rahoton Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka a watan Satumba na shekarar 2024 ta ce, ba a ware dala daya daga cikin dala miliyan 60.8 da aka yi amfani da su wajen ɗaukar nauyin kwaroron roba da magungunan hana haihuwa da hukumar ta raba a duk duniya da aka ware wa yankin Falasɗinu ba.

Haka kuma rahoton ya nuna cewa, magungunan hana ɗaukar ciki da aka aika zuwa Gabas ta Tsakiya, an raba wa gwamnatin ƙasar Jordan ne.

Andrew Miller, tsohon jami’in ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Biden wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin sakataren harkokin Isra’ila da Falasɗinu, ya shaida wa jaridar Times ta Isra’ila a ranar Laraba cewa ikirarin Leaɓitt “ƙarya ne” kuma “ɓatanci mai zafi” a ɓangaren sabuwar gwamnatin. .

“Ta yiwu an ware dala miliyan 50 don lafiyayyar mu’amala ko wani abu da ya dangance shi, wanda zai haɗa da ilimin mata da sauran ayyuka da yawa, amma tabbas ba kwaroron roba kaɗai ba,” inji shi.