Aƙalla mutane 15 daga cikin masu ziyarar addinin Hindu suka mutu sakamakon turmutsutsun da aka samu yau Laraba, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Tuni Firaminista Narendra Modi ya aike da saƙon ta’aziya ga iyalan waɗanda haɗarin ya ritsa da su.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan turmutsutsun ba a bukukuwan addinin mabiya Hindu da ke gudana a Kumbh Mela ta ƙasar Indiya, wanda ke samun halartar mutane aƙalla miliyan 4 kowaccce shekara.
Rahotanni sun ce an samu haɗarin na ranar da asubah lokacin da dubban mutane suka kwarara domin yin wanka a kogin Ganges wanda ake girmama ruwansa, inda suka dinga take mutanen da ke bacci kusa da shi.
Wani daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya, Renu Deɓi, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mutane da dama ne suka danne shi amma Allah ya kuɓutar da shi.
Devi ya ce dattawa da mata da dama sun mutu saboda babu wanda ya kai musu ɗauki lokacin da lamarin ya auku.
Wani likita a asibitin wucin gadi na garin ya tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 15, tare da samun wasu da dama da suka samu raunuka daban-daban.
Ranar ta Laraba na ɗaya daga cikin ranaku masu daraja ga mabiya addinin Hindu da ke halartar wannan ibada, inda limaman suke jagorantar mahalarta wajen wanka a wannan kogi na Ganges mai daraja.