Barau Jibrin ke kitsa duk wani ruɗani a siyasar Kano ba Ganduje ba – Jaafar Jaafar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shahararren ɗan jaridar nan, kuma mamallakin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya zargi Mataimakin Shugaban Majisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano.

Jaafar Jaafar ya bayyana hakan ne a cikin shirin “Fashin Baƙi” da suke gabatarwa a duk ranar Lahadi tare da Lauya, Abdu Bulama Bukarti, Lauya Abba Hikima , ɗan jarida Nasiru Zango da kuma Naziru Mika’il.

A cewar Jaafar “Mutane da yawa suna tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Su na shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi.

“Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗan sanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu.

“Irin wannan bai kamata ba. Ko takarar gwamna mutum zai yi, bai kamata ya kassara al’umma ba. Irin wannan bai dace ba, ba kuma kishin jiha da al’umma ba ne,” inji Jaafar Jaafar.

Sanata Barau wanda shine mataimakin shugaban majalisar dattawa, na kan gaba wajen nuna maitarsa ƙarara na neman fafatawa da gwamnan Kano Abba Yusuf a 2027.

Sai dai kuma kamar akwai jan aiki gabansa domin suma mutanen gwamnatin sun wasa wuƙaƙensu suna jiransa da kuma jiran lokaci.

By ukarofi