Mun samu nasarori da dama cikin ƙanƙanin lokaci – Gwamnan Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana irin nasarori da gwamnatinsa take samu a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa a zama na 24 a ranar Laraba a Fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bada tallafin kayan makaranta ga ɗaliban firamare a matakin farko da suka amfana daga ƙananan hukumomi 44 dake jihar.

Ya kuma bayyana cewa akwai batun biyan Naira biliyan 5 na ƙarin kudin ‘yan fansho bayan biyan abinda yakai Naira biliyan 16 a baya.

“Mun yi aikin bada tallafin dabbobi ga mata da muka saba yi karo na uku da bai wa Matasa suma shanu da raguna ƙarƙashin Shirin da Bankin Duniya da yake bada tallafi, wanda ma’aikatar Kula da Noma da Hukumar KNARDA suke kula da shi.”

“Sannan mun yi ƙoƙari wajen bude titunan kilomita biyar-biyar a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dawakin Kudu wanda yake a tsarin Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne a lokacin da yana gwamnan Kano”, inji Abba.

Gwamnan ya bayyana batun yaye ɗaliban Bagauda da aka yi cikin makwan nan bisa ƙoƙarin Gwamnatin na sama wa matasa aikin yi da za su dogara da kawunansu a matsayin ɗaya daga cikin alƙawuran da suka ɗauka wa al’ummar jihar.

“Akwai jarin mata da mu ke badawa duk ƙarshen wata a kaf faɗin Jihar Kano Kananan hukumomin 44 wanda a wannan tsari muka ɗauki mata 100 kowacce ƙaramar hukuma sai 200 daga ƙananan hukumomin dake cikin birni,” inji shi

Haka kuma Gwamnan ya bayyana nasarar buɗe Makarantar Koyar da ɗinki dake Karamar Hukumar Kura bisa tabbatar da cigaba da koya wa matasa sana’a.

Har’ilayau, gwamnan ya yaba wa sababin kwamishinonin da ya naɗa bisa ƙoƙarin da suka fara wajen gudanar da aiki bisa yadda ya kamata tare da ƙara ƙarfafa musu gwiwa.

By ukarofi