Gwamna Buni ya jaddada bai wa sojoji gudunmawar kawo ƙarshen Boko Haram 

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu 

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya jaddada bai wa sojojin Nijeriya ma su aikin samar da tsaro a jihar cikakkiyar gudunmawa da goyon baya domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addancin ƙungiyar Boko Haram a jihar.

Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a tsakiyar wannan mako, a sa’ilin da Babban Hafsan Sojojin (COAS), Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya Kawo masa ziyara a fadar gwamnatin jihar dake Damaturu. 

Har wala yau kuma, Gwamnan ya yaba wa sojojin bisa ga jajircewarsu wajen tabbatar da samun gagarumin ci gaba ta fuskar bunƙasar tsaro a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa a cikin ilihirin ƙananan hukumomin jihar 17 a jihar, an samu ci gaba sosai a fannin tsaro, yayin da al’umma ke ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin walwala.

“Ci gaba da aka samu ta fuskar tsaro a faɗin wannan jihar ya baiwa gwamnati damar aiwatar da manufofi da tsare-tsare don inganta rayuwar al’umma ba tare da wata tangarɗa ba.” In ji Buni.

A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran ɓangarorin jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin daƙile shigowar yan ta’adda cikin jihar.

A nashi ɓangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki ɗaya.

“Babban burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo ƙarshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri,” inji COAS.

Hakazalika kuma, ya bayar da tabbacin cewa zai yi amfani da hazaƙa tare da ƙwarewarsa- musamman yadda a baya ya yi aiki a jihar Yobe- domin kawo ƙarshen matsalar yan ta’adda.

Haka kuma, Janar Oluyede ya yaba wa gwamnatin jihar Yobe bisa cikakken goyon baya tare da irin yadda take tallafawa rundunar sojojin Nijeriya a kowane lokaci tare da yin kira kan ci gaba da ƙoƙarin da take na baiwa sojojin tallafin don sauƙaƙa musu ayyukan aikin yaƙi da matsalolin tsaro.

By ukarofi