Gwamnatin Tarayya ta sanar da mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta zaɓi 16 a matsayin mafi ƙarancin shekerun neman gurbin shiga manyan makarantu a faɗin Nijeriya.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya sanar da sabon sauyin a ranar Litinin, yayin zaman tsare-tsaren Hukumar kula da bada gurbin karatu ta JAMB a Abuja.

Ya ce, a baya ana amfani da 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun, wanda a yanzu an yi wa tsarin garambawul, lamarin da ya shigo da sabon tsarin.

Dakta Alausa ya kuma ce, duk makarantar da aka samu ta ƙi bin sabon tsarin shekarun, za ta fuskanci hukunci mai tsauri.

Kazalika, ya jaddada aniyar gwamnatin ta sanya lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) acikin hanyoyin neman gurbin karatu, lamarin da acewarsa zai taimaka wajen rage shigar da shekarun ƙarya da wasu haramtattun ayyuka cikin tsarin.

Haka kuma, ya gargaɗi makarantun da ke ɗaukar ɗalibai karatu ta wajen tsarin da ta amince da shi na ‘Central Admission Processing System’ (CAPS), yana mai cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’ida kuma za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikatawa.

By Babaji