Marubuci tamkar likita ne, yana duba cutar da ta shafi zamantakewar al’umma – Jibrin Yusuf Kaila 

Spread the love

“Abin takaici ne yadda marubuta ke amfani da fasahar AI wurin ƙirƙiro labari”

Daga JIBRIN YUSUF KAILA 

A kowanne zamani ana samun cigaba ta fannoni daban-daban a ɓangaren rubutu ko a rayuwar marubuta, wanda silar hakan ke bada damar haɓɓaka adabi a rayuwar ɗan’adam. Kodayake wani lokaci cigaban na zuwa ne ta fuskoki daban-daban, akwai amfani da rashin sa. 

Ga mai nazari da kuma lura zai fahimci cewa, kafin marubuci ya fara cin moriyar rubutun da yake yi, yana buƙatar amfani da wasu abubuwa da dama. Daga ciki, akwai bincike da nazari. Lallai kowanne cikakken marubuci ya yi nazari kan abin da yake son ya yi rubutu a kai, da kuma hanyoyin da suka dace ya yi rubutun, kamar yadda yake a rayuwar marubutan da suka gabace shi, wannan yana da muhimmanci sosai. Babu wani marubuci da yake samun riba da ɗaukaka ba tare da koyi daga abin da wasu marubuta na baya suka yi ba, kamar yadda marubuci ba ya taɓa zama cikakken marubuci sai ya yawaita karanta rubuce-rubucen wasu. 

Kwanakin baya, marubuciya Hajara Ahmad Maidoya, ta taɓo wani batu mai muhimmanci, game da masu sharhi akan abin da ya shafi marubuta da rubuce-rubuce. Tabbas, tattaunawa akan irin waɗannan muhimman batutuwa na da kyau, saboda sabbin marubuta masu tasowa su yi koyi akai. Domin rashin nazari na iya gurgunta baiwar rubutu da marubuci ke da ita. 

Marubuci tamkar Likita yake, Sai dai shi ba tiyata ko ƙwayoyin magani ko kuma jinya yake yi ba, yana duba cutar da ta shafi zamantakewar al’umma ne, sai ya ba da magani ta hanyar shawarwari da misalai daga rayuwar wasu ta cikin labari irin na hannun ka mai sanda. A yayin da marubuci ya gano wata cuta a tunani, ko ra’ayi, halayya, ko a ɗabi’ar mutane da ke hana su cigaba, ya kuma kawo magani ta hanyar zurfafa tunani da kalmomi masu ma’ana da jan hankali. Mutumin da yake da irin wannan baiwar, ba ƙaramin mutum ba ne, domin baiwar ilimi da rubutu, aba ce mai matuƙar daraja. 

Sai dai abin takaici ne yanzu za ka ga marubuci yana amfani da fasahar zamani ta AI ko ChatGPT wajen rubuta labari, a maimakon zurfafa tunani da amfani da baiwar ƙirƙira da Allah Ya bashi. Haƙiƙa dogara da wata na’ura wajen ƙirƙiro da labari gazawa ce gare shi, kuma tabbas hakan zai iya dakushe masa tunani da basirar da Allah Ya ba shi.

Ya kai ɗan’uwa marubuci, wanda yake da wata baiwa, wanda ba kowa yake bai wa ba, ka yi taka tsantsan ga yawan amfani da AI (Artificial Intelligence) wajen umartarsa ya baka ƙirƙirarren labari, wanda sau da dama rubutun ba ya inganci, Hausar ba ta fita da kyau, kuma tasirin labarin ba ya fita da kyau.

Ga sababbin marubuta kuwa amfani da AI zai iya dakushe wa marubuci baiwar sa, domin ba zai ba mutum dama wajen nazarce-nazarce akan adabi ko yawaita karance-karancen littattafai ko labarai ba, silar haka zai sa shi kasala a ƙirƙiro labari da karance-karance littattafai da bincike. Zai sa masa ƙyuyar yin rubutu, da girman kai, yadda zai riƙa jin shi ma daidai yake da kowanne marubuci. 

Sai dai ka sani, ya kai marubuci. Ba Ina nufin cewa amfani da fasahar AI ko ChatGPT ba shi da wani amfani ba ne, amma zance na gaskiya akwai kuskure babba wajen dogaro da shi don ya ƙirƙiro maka rubutun labari. Ga wanda ya san rubutu kuma ya san garɗi da daɗin yadda marubuta ke sarrafa labari cikin hikima da adon harshe, idan yana karanta labarin da AI ya tsara zai ji tamkar miya ce babu gishiri, don labari ne cikin gwaranci kuma ba ma’ana.

Zancen Gaskiya:

Marubuci ba kawai mai riƙe da alƙalami ko na’ura ba ne, marubuci mutum ne mai fahimta da iya haskaka zuciya da hangen nesa. Mai iya tsara tunani daga cikin zuciyarsa, ya jujjuya shi zuwa kalmomi masu ƙayatarwa. Mai sarrafa harshe da iya fassara abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma zuwa kyakkyawan salo na ilmantarwa ko nishaɗi.

Idan wannan duk AI ne ke yi maka, kai kuma baka da wani ƙarin basira sai ba da umurni: “Ka rubuta min labari,” lallai ka yi rashi a matsayin ka na marubuci.

Illar Dogara Da AI A Rubutu:

1. Lalata Basira – Kana rage ƙarfin tunani da haɓakar fasahar rubutunka.

2. Zubar da Salonka na Asali – Kowanne marubuci yana da salonsa na musamman. Amma idan AI ke tsara maka komai, baka da salo sai abin da AI ya baka.

3. Mayar da Kanka Maƙaryaci – Kana nunawa jama’a cewa kai ne ka rubuta, alhali ƙarya ce. Wannan ya saba da ɗabi’ar gaskiya ta marubuta na haƙiƙa.

4. Zubar Wa Kanka da Daraja – Idan aka gano duk rubuce-rubucenka daga AI ne, ba za ka sake samun ƙima a idon ƙwararru da masu karatu ba.

Amfanin AI Ga Marubuci: Yi amfani da shi wajen nazari, bincike ko gyara, ba sai ya rubuta maka komai daga tushe ba. Ka rubuta da kanka, sannan sai ka nemi taimakon AI don ganin yadda za ka iya inganta shi, amma kar ya maye gurbin tunanin ka.

Matuƙar kana bai wa AI duk rubutunka ya yi maka to, KAI BA MARUBUCI BA NE!

By ukarofi