Daga MUHAMMAD ILIYASU (MD Asnanic)
Mawaƙi: Aminu Ladan Abubakar (ALA)
Mai gabatarwa: MD Asnanic
Shimfiɗa:
Da iznin Ubangijin da ke ba da aron dama, wannan sharhi namu na yau ya zo da zummar sharhantar ɗaya daga cikin waƙoƙin fasihin mawaƙin Hausar nan na Arewa, shugaban kamfanin Hikima Multimedia, Alan waƙa. Cikin wata waƙarsa mai cike da jan hankali, mai taken ‘So Sarƙaƙƙen Zance’. Ku biyo ni mu tsunduma cikin sharhin.
Gangar jikin waƙa:
Amshi:- So sarƙaƙƙen zance mai sarƙaƙe masoya, So soso na kankan mai sissille masoya.
1. Allah kai muke so, So mai sadar da sawaba.
Ya sarkin salama, mai son ka ba zai same ba. So fa halitta ce, ba harsashe ba ne ba.
Zaɓen so zuciya ne, ba tilasshi ake ba.
So alƙawari ne, ba hilata ake ba.
So fa gamon jini ne, ba gamo na gambiza ba.
Kamar sartse yaka suka, ba sukar mashi ba.
Kamar maiƙo yaka naso, ba dira-ta-ungula ba.
Linzamin so ilimi ne, ba tarin jahilci ba.
Turken so hankali ne, ba biye wa son rayi ba.
Komai zafi laƙaninsa, haƙuri ba zai gaza ba.
So ya zama cuta, haƙƙuri fa ba illa ba.
Ku mu ankara dai masoya, ba sambatu nake ba.
Ba sambatu nake ba, ba jinini nake ba.
2. So ba kwarmato ba, So ba kwakwazo ba.
So ba kwakwazo ba, bambaɗo ba.
So ba kankanba ba, ai nazari samari so ba bambaɗo ba.
3. So ba kwarkwasa ba, So ba zirgilli ba.
So ba tsugudidi ba, ba da giringiɗiishi ba.
So ba shisshigi ba, albishirin ku masoya so ba kinibibi ba.
4. Ba gutsiri-tsoma ba, ba tsegunguni ba.
Ba surkulle ne ba, So ba tsafi ba.
Ba yin tsatsuba ba, ai nazari masoya so ba bin bokaye ba.
5. Ba bin bango ne ba, ba shan minti ba.
Ba nanaye ba, ba cika lubaye ba.
Ba gwalli ba ne ba, albishiri masoya ba zuƙi-tamalle ne ba.
6. kar ki sake, Kar ki sake ai maki nanaye.
Kar ka sake, Kar ka sake ai maka lubaye.
Da kin gan shi, ki dube shi ki nazarin ɓoye.
Da ka gan ta, ka dube ta kai nazarin waye.
So ba cin fuska ba, kuma ba cin zarafi ba.
ɗaiɗaikun Kalmomi:
Sawaba – sauƙi ko sakamako.
Same (samewa) = Asara
Harsashe (hasashe) = Zato
Tilasshi =Tilastawa
Hilata (hila) =Yaudara ko Zamba
Sambatu =zance cikin rashin hayyaci
Jinini =Cecekuce ko sambatu akan abinda ya wuce na ɓacin rai
Kwarmato =Surutai mara amfani ko ihu.
Kwakwazo =Duk ɗaya ne da kwarmato
Kankanba = Karambani
Kwarkwasa = Aiki ko zance mai jan hankali a soyayya
Tsugudidi = ɗaukar magana daga wannan bagire zuwa wancan
Kinibibi =Annamimanci ko algungumanci
Tsegunguni =Jami’in tsegumi
Gwalli =girman kai, ko yin abu don jin daɗi
Zuƙi-tamalle = ƙarya
Bambaɗo = Bambaɗanci (roƙo)
Zirgilli = ƙarya ko wuce gona da iri.
Tambihi/Sharhi:
Wannan waƙa za ta iya kasancewa mai wahalar fahimta ga mai ƙarancin nazari ko kuma wanda ba Bahaushe ba, ta zo da sarƙaƙiya da kuma wani irin salo mai wahalar fahimta.
A zahirance, fasihin mawaƙin ya yi bayani ne a kan so, ta yadda yake ƙoƙarin nuna cewa shu’umin abu ne, kamar ma’arifa ce duk yadda ka fahimce shi to a wajen wani ba haka yake ba. Haka ne ya sa yake ta cewa “So ba kaza ba ne, So ba kaza ba ne” sannan kuma bai faɗi menene son ba. A taƙaice dai So yana da wuyar sha’ani.
Tabbas, za mu iya kiran wannan waƙa da ɗan ƙaramin kundi na fayyace haƙiƙanin so, musamman idan muka yi la’akari da gamsasshen bayanin da mawaƙin ya yi duk da yana cike da sarƙaƙiya.
Waƙar ta yi wahalar fahimta ne saboda abinda aka waƙe shi ma mai wahalar fahimta ne.
Salo/Tsari:
Komai na wannan waƙar mai wahalar ankarowa ne, hatta salonta ma a cukurkuɗe yake don tsabar azanci da zalaƙa. Da farko dai tana da salon ƙafiyar ‘ba’ a kowane ɗango da faɗuwar baiti, in banda wasu ɗangwaye na baitin ƙarshe da suke da ƙafiyar ‘ye’. Haka zalika hatta baitukan ma ba girmansu caya ba, ta yadda baitin farko yana da ɗango sha huɗu, baiti na biyu da na huɗu suna da ɗangwaye hurhuɗu (4), baiti na uku da na biyar kuwa suna da ɗangwaye uku-uku, ta yadda baitin ƙarshe na shida ke da ɗangwaye biyar. Jumullar baitukan waƙar baituka shida ne.
Jigo:
Jigon waƙar bayyananne ne tun daga kan amshin waƙar, wato so sarƙaƙƙen zance ne, kuma idan muka yi la’akari da maganganun cikin waƙar za mu iske haka, ‘so ya zarce gayar tunani, sai mahaliccin son ne kawai ya san maƙurarsa.
Tarihin Mawaƙi:
Aminuddin Ladan Abubakar (ALA) ko Alan waƙa, an haife shi a shekarar 1974 cikin unguwar yakasai ta birnin Kano.
Ya yi karatun primary a unguwar Tudun Murtala daga 1980 zuwa 1986, daga nan ya wuce makarantar secondary ta Dakata daga 1986 zuwa 1992. A daidai wannan halin ne ya sami tsaiko bai cigaba da karatu ba sabo da yana yin rayuwa. Sannan ya yi karatun addini mai zurfi kama tun daga gidansu har zuwa fa malamansa. Sannan a wannan lokacin da ya kammala secondary ne ya fara rubutu sannan daga baya ya shiga harkar waƙa, duk da cewa waƙar ita ya fara yi tun yana islamiya a mumbarin maulidai (waƙar yabon Annabi). Sai dai waƙarsa bata fara shiga kafafen yaɗa labarai ba sai a shekarar 2003.
Rubutun ƙagaggen labari kuwa ya fara shi tun a 1992, yayin da ya fara wallafawa a 1999.
Aminu ALA ya sha gwagwarmaya sosai a fannin waƙa wanda har sai da ta kaishi ga shiga gidan maza.
