Ogun: ‘Yan sanda sun ceto ƴan Kamaru 38 da aka rufe a wani gida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Ogun, ta yi nasarar ceto wasu ƴan ƙasar Kamaru guda 38 bayan rufe su da aka yi a wani gida dake yankin Mowe a jihar.

Mutanen sun haɗa da maza 22 da mata 16 waɗanda wasu ƴan damfara suka yaudare su da sunan za su sanya su a manyan harkokin kasuwanci.

Wani shaida ya faɗa wa manema labarai cewa, an ceto su ne a yayin sintirin jami’an na ranar Lahadi, inda aka gano su a wani ƙauye mai suna Adesan Abule a sakamakon jin surutun mutane daga gidan da aka rufe su.

A yayin haka ne ƴan sandan suka shiga gidan inda suka same su a ɗaure cikin mawuyacin hali.

Wata majiya daga ƴan sanda ta ce, mutanen sun taho ne daga Kamaru da nufin zuba jari a wani harkar kasuwanci da ake kira da ‘Quinnet’.

Sun kuma ce, maƙudan kuɗaɗe suka biya ƴan damfarar domin shiga cikin harkar.

An yi nasarar kama wani ɗan Anambara, wato Ndubusi Awereobi mai shekaru 35 a wajen da aka ceto mutanen, wanda a halin yanzu ana gudanar da bincike akansa.

By Babaji