Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin neman kirkiro Jihar karaɗua Alhaji Kabir Aliyu ya miƙa takardun buƙatar neman jihar ga kwamitin ƙirƙiro jihohi na Majalisar Dattijai da na Wakilai.
Yace wannan ba shine karo na farko ba da suka miƙa buƙatar ne man jihar karaɗua ba,sun miƙa wannan buƙata a shekarar 1995,2011 da 2021.
Alhaji Kabir Aliyu ya bayyana wa manema labarai cewa sun cika duk ƙaidoji da ake nema na ƙirƙiro jihar karaɗua.
Ya ce yankin karaɗua na da ƙananan hukumomi 11 a Jihar Katsina, kuma da zarar sun sami jihar za su ƙara sabbin ƙananan hukumomi guda 11
Sakataren kwamitin injiniya Tukur Lawal Funtua ya ce buƙatar neman ƙirƙiro jihar karaɗua na daidai da tsarin mulki na ƙasa.
Ya bayyana cewa wannan buƙata na neman ƙirƙiro Jihar karaɗua yayi daidai da buƙatar al’ummar yankin.
Injiniya Tukur Funtua sai yayi kira ga al’ummar yankin da sunada cikakken goyon baya wajen fafutikar neman jihar karaɗua.
“Kowa yasan yankin karaɗua yanki ne na harkokin kasuwanci da noma,har idan wannan buƙata ta tabbata cikin lokaci kaɗan jihar karaɗua zata yi gogayya da sauran jihohi”injiniya Tukur Lawal Funtua ya ce.
