Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Tsohon Ministan Sufuri, Sanata Abdullahi Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ce za ta jagoranci ceto Najeriya daga halin matsin tattalin arziki da rashin shugabanci, tare da mayar da jam’iyyar APC jam’iyyar adawa a babban zaɓen 2027.
Idris ya bayyana haka ne a wani babban taron haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da aka gudanar a ɗakin taro na Shugleez Event Centre da ke Gombe, inda wakilan jam’iyyun adawa daga sassa daban-daban na jihar suka hallara domin cimma matsaya guda.
Ya ce, “Haɗin guiwar da muke yi ba wai kawai don karɓar mulki ba ne, amma don ceto ƙasa da talakawanta daga ƙangin matsalolin da ke addabar su.”
A yayin taron, jam’iyyu masu adawa sun amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasar haɗin gwiwa da za su yi amfani da shi wajen fuskantar zaɓe mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, Auwal Abba Barde, ya bayyana cewa jam’iyyar na karɓar sabbin mambobi a kai a kai, tare da tabbatar da cewa za a ba su wakilci da dama a harkokin jam’iyyar.
An kafa kwamitin rajista da za ta jagoranci shiri da tattara sabbin ‘yan jam’iyya ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar Gombe, John Lazarus Yoriyo, tare da AVM Adamu Fura a matsayin mataimaki.
A nasa ɓangaren, tsohon shugaban matasan APC, Sunusi Abdullahi Ataka, ya ce wannan haɗakar na da matuƙar tasiri wajen ƙwato mulki a matakin jiha da ƙasa.
Fitattun ‘yan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da wakilin tsohon Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami, Abubakar Abubakar BD, da wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa daga faɗin jihar.
