Daga USMAN KAROFI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Najeriya ba ta da wani buri na mallakar makaman nukiliya, kasancewar burinta yanzu shi ne yaƙar talauci da sauyin yanayi. Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin sakataren hukumar CTBTO, Dr. Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shettima ya jaddada cewa Najeriya na goyon bayan cikakken haramta gwajin makaman nukiliya a duniya, tare da godiya ga CTBTO bisa jajircewar da ta ke yi wajen sa ido da kare lafiyar muhalli.
Dr. Floyd ya yaba da rawar da Najeriya ke takawa a wannan fanni, musamman ta hannun hukumar kula da makaman Nukiliya (NAEC) da hukumar kula da tsaro na Nukiliya (NNRA). Ya ce bayanan da Najeriya ke samarwa na taimakawa wajen gano annoba da sauran bala’o’in halitta kafin su faru, wanda hakan ke ceton rayuka.
A nasa ɓangaren, shugaban NNRA, Dr. Yau Idris, ya bayyana hadin gwiwar Najeriya da CTBTO a matsayin wata hanya ta tabbatar da bin dokokin kasa da kasa wajen haramta gwajin makaman nukiliya.
A wani taron daban da aka gudanar a Abuja, Shettima ya jaddada muhimmancin tsarin shari’a mai inganci wajen bunƙasa kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron bita na kwana biyu ga alƙalai da hukumar SEC ta shirya. Ya ce gaggawar yanke hukunci cikin adalci da fasaha na ƙara jawo jari da amincewa daga masu zuba hannun jari, wanda zai taimaka wajen cigaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Haka kuma, Shugabar alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta ce kasuwar hannun jari ta zama hanya ta ƙarfafa tattalin arzikin al’umma. Ta ce alƙalan Najeriya suna da rawar da za su taka wajen kare amincin kasuwa daga damfara da cin hanci. A ƙarshe, shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta gurfanar da kamfanoni 58 masu gudanar da ayyukan zamba na tsarin “pyramid” a gaban kotu tare da samun nasarar gurfanar da biyu.
