Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba baƙi ba ne, kuma ba sabbin shiga ba ne. A cewarsa, “Fiye da kashi 90 cikin 100 na masu aikata ta’addanci daga yankinmu suke. Mun san iyayensu, kakanninsu, kuma muna zaune tare da su.” Ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Talata.
Gwamna Raɗɗa ya ce matsalar tsaro ita ce babbar tangarda ga cigaban Jihar Katsina. Duk da cewa gwamnoni na zaman shugabannin tsaro a jiharsu, ya bayyana cewa rundunar soji da ‘yan sanda na aiki ne bisa tsarin su na daban.
Don haka ne gwamnatin jihar ta ƙirƙiro wata ƙungiya ta matasa daga yankunan da ake fama da ta’addanci, domin su bayar da gudunmawa wajen yaƙi da ‘yan bindiga.
A cewarsa, “Wannan yaƙi na buƙatar al’umma su shiga ciki. Saboda haka muka ƙirƙiri wannan rundunar don su ba da bayanai daga cikin gari. Su ne za su iya kai hari inda ‘yan bindiga ke ɓoye, su gano masu ba su bayanai da tallafi.”
Ya ce har sai an yanke wannan kushewar cikin gida, ba za a iya magance matsalar tsaro gaba ɗaya ba.
