JAMB ta mayar da 150 mafi ƙarancin makin shiga jami’a ga ɗalibai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da lamuran bada gurbin garatu ga ɗalibai (JAMB) ta ayyana 150 a matsayin mafi ƙarancin makin ɗaukar ɗalibai karatu a baki ɗaya jami’o’in Nijeriya.

A yau Talata ne JAMB ta yi hukuncin a yayin zama na tsare-tsaren jarrabawa na 2025, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu dake Abuja.

Ta kuma zaɓi 140 a matsayin mafi ƙarancin makin samun gurbin karatu a makarantun kwalejin ungozomanci, wato ‘colleges of nursing’, sai kuma maki 100 ga makarantun kwalejin noma da na ilimi.

A wani saƙo da ta wallafa ta kafar X, hukumar ta ce matakin zai fara aiki ne daga zangon karatu na gaba.

Gwamnatin Tarayya a nata ɓangaren, ta ayyana shekaru 16 a matsayin mafi ƙaranci ga ɗaliban da ke neman shiga jami’a.

By Babaji