Gwamnatin Tarayya ta sanar da taken ranar bikin ’yancin kan Nijeriya na cika shekara 65

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin tarayya ta sanar da taken bikin ranar samun ‘yancin kai na Nijeriya a shekarar 2025.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya raba wa Blueprint Manhaja ranar Laraba a Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana babban jigon bikin cikar ‘yancin kai na 2025, mai taken: Nigeria @ 65: All Hands on Deck for a Greater National na nuni da buƙatar haɗin kai, da kishin ƙasa a tsakanin cibiyoyin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula, da ’yan ƙasa don ciyar da ƙasa gaba da zaman lafiya, wadata, da ci gaba.

Gwamnatin ta ce zaɓar taken ya nuna irin juriyar da Nijeriya ta samu tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, inda ta jaddada muhimmancin ƙarfafa nasarorin da aka samu a baya tare da ci gaba da cimma muradu mafi girma a ƙarƙashin ajandar sabunta fata.

Ana sa ran hukumomin gwamnati da abokan hulɗa za su daidaita shirye-shiryensu da taken bikin tunawa da ranar tunawa da saƙonsa a dukkan ɓangarori na rayuwar ƙasa.

A wani ɓangare na ayyukan da aka shirya domin bikin samun ‘yancin kai karo na 65, za a gudanar da sallar Juma’a a ranar Juma’a, 26 ga watan Satumba, sannan za a gudanar da taron coci-coci a ranar Lahadi 28 ga watan Satumba.

Haka kuma za a yi taron manema labarai na duniya a ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ana gudanar da taron manema labarai na duniya a ranar Litinin, 29 ga Satumba

By ukarofi