Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Tajudeen Abbas ya jaddada goyon Majalisa ga tsare-tsaren karɓo rance na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tajudeen ya ce, Majalisar Wakilai na tare da tsarin Tinubu, yana mai bayyana karɓo bashin da wata dabara ta bunƙasa tattalin arziki da kawar da talauci.
Tajudeen ya faɗi hakan ne a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO) karo na 8 wanda ya gudana a Abuja.
Ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Majalisar ta ƙi amincewa da tsarin ciyo bashin Tinubu, yana mai kiran irin waɗannan rahotannin da “na yaudara da ƙarya.
“Mutane sun fassara jawabin da Shugaban Masu Rinjaye ya yi a taron Majalisun Afirka ta Yamma (WAPC) ba daidai ba, aka yi ta yada labarin cewa Majalisar Wakilai ba ta goyon bayan ciyo bashin Gwamnatin Tinubu.
“Wannan ba gaskiya ba ne, yaudara ce kawai domin Majalisar Wakilai ta 10 ta sha nanata matsayarta cewa duba da buƙatuwar da ake da ita, karɓo bashi na da matuƙar muhimmanci.
“Duba da yadda zamani ya sauya, dole ne Nijeriya ta ciyo bashi domin gina manyan ababen more rayuwa, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma kare masu rauni.
“Abu mafi muhimmanci shi ne, Shugaban ƙasa ya tabbatar mana cewa duk wani rance zai kasance mai manufa tare da bin ingantattun ƙa’idodin duniya,” inji Abbas.
Ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa rancen da Shugaba Tinubu ke karɓo wa bai wuce ƙa’ida ba kuma ana amfani da kuɗin wajen gina ababen da za su taimaki jama’a.
Tajudeen ya ce, Ofishin Kasafin Kuɗi da Bincike na Majalisar Dokoki (NABRO) da aka kafa zai samar da bincike mai zaman kansa kan rance, ɗorewar basussuka da kuma manufofin kuɗi.
Kakakin Majalisar Wakilai ya aara da cewa, duk da karɓo bashi na da muhimmanci, rufe hanyar ɓarna, rashawa da sulalewar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba ma ya zama dole.
A cewarsa, Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 18 a kowace shekara sakamakon laifuffukan kuɗi, wanda ya kai kusan 3.8 na tattalin arzikin ƙasar.
