Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar da ke Kula da Gidajen Yari ta Nijeriya (NCoS) ta kama wani mutum mai suna Njimogu Ikedi da laifin yin yunƙurin safarar hodar Iblis da sauran muggan ƙwayoyi zuwa gidan yarin Kuje a babban birnin tarayya Abuja.
Kakakin hukumar NCoS, Samson Duza ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Duza, wanda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:45 na yammacin ranar Asabar a yayin da ake gudanar da bincike na yau da kullum, ya bayyana wanda ake zargin a matsayin Njimogu Ikedi, wanda ya “ɓoye wasu abubuwan da ake kyautata zaton hodar iblis ce da wasu ƙwayoyi a cikin tufafinsa yayin da yake ƙoƙarin ziyartar wani fursuna.”
A cewarsa, Konturola na hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja, Christopher Jen, ya bayar da umarnin kamo wanda ake zargin, inda ya ƙara da cewa tuni aka miƙa wanda ake zargin ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, domin bincike da gurfanar da shi gaban kotu.
Jen ya gargaɗi maziyarta da su guje kai wa fursunoni muggan abubuwa, ya ƙara da cewa jami’an tsaro za su riƙa bankaɗo irin waɗannan ayyukan.
Ya kuma roƙi jama’a da su taimaka wa hukumar wajen gyarawa da gyara masu laifi domin kare lafiyar jama’a.
Wannan lamari ya zo ne fiye da shekara guda bayan da aka kama wata mata tana yunƙurin yin fasa kwaurin ƙwayoyi a cikin gidan yarin.
Matar, wacce ta yi iƙirarin cewa an aike ta ne domin ta kai wa wani fursuna da ke wurin magungunan, ta yi kama da baƙuwa sannan ta ɓoye ƙwayoyin a cikin abinci.
Wannan lamarin ya biyo bayan wani lamari makamancin haka a watan Yulin 2024, lokacin da aka kama wata mata da laifin yunƙurin shigo da ƙwayoyi zuwa cikin wurin.
