Gwamnatin Tarayya za ta kafa Cibiyar Karɓar Gudummawar Jini a ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ana shirye-shiryen gina cibiyar tattara gudunmawar jini a dukkan ƙananan hukumomi 774, ciki har da gundumomin Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.

Sanarwar ta ce za a kafa Cibiyoyin Bayar da Gudummawar Jini (Blood Collection Centres) ne domin a tabbatar kowace cibiyar kula da lafiya da asibitocin ƙasar su na samun wadataccen jinin da marasa lafiya ke buƙata.

Kakakin Yaɗa Labaran Cibiyar Tattara Jini ta ƙasa (NBSA), Abdullahi Haruna ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Asabar, a Abuja.

Sanarwar ta ruwaito Babban Daraktan NBSA, Saleh Yuguda na cewa gwamnatin tarayya ta ƙudirta magance matsalar ƙarancin jini a faɗin ƙasar nan, domin idan aka yi wannan gagarimin aiki a faɗin ƙasar nan, za a ceci rayuka masu ɗimbin yawa.

“Muna aiki haiƙan domin tabbatar da cewa an magance matsalar ƙarancin jini. NBSA ta haɗa guiwa da ƙarfi tare da Hukumar Tsaro ta NSCDC domin kafa rumbun tara jini a ofishin NSCDC.

“Za a yi hakan ne domin magance ƙarancin jini a lokutan kai ɗaukin gaggawa.

“Saboda wannan shiri na kafa Cibiyoyin Karɓar Gudummawar Jini a ƙananan hukumomi 774 na ƙara tabbatar da irin shauƙi da ƙwazo na wannan gwamnati wajen inganta fannin kiwon lafiya,” inji shi.

By ukarofi