Gwamnan Bauchi ya kori kwamishinan lafiya tare da soke ma’aikatar ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya sauke Dakta Adamu Sambo daga muƙaminsa na kwamishinan lafiya.

Sanarwar ta zo ne a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, 2024, a yayin bikin rantsar da sabbin kwamishinonin guda uku da babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro a gidan gwamnati da ke Bauchi.

Ya bayyana cewa an sauke Dr Sambo ne a wani ɓangare na ƙoƙarin garambawul ga gwamnatin, inda ya tabbatar da cewa zai sake neman wani muƙami ga tsohon kwamishina a gwamnati.

Gwamnan ya kuma ce ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu ba za ta samu sabon kwamishinan da zai maye gurbin Ahmed Aliyu Jalam da ya rasu a wani hatsarin mota kwanan nan ba, duba da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Ya ce ma’aikatar ƙananan hukumomin za ta kasance ƙarƙashin babban sakatare.

Babbar mai shari’a a jihar, Mai shari’a Rabi Talatu Umar, wadda mai shari’a Faruk Umar Sarki ta wakilta, ta rantsar da sabbin kwamishinonin uku da aka naɗa kafin a fara taron majalisar zartarwa ta jihar.

Su ne Hajiya Zainab Babantakko, wadda aka tura ma’aikatar harkokin mata ta maye gurbin Hajiya Hajara Jibrin Gidado, wadda aka zaɓe ta a matsayin shugabar zartaswar ƙaramar hukumar Itas Gadau a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a kwanakin baya; Dr Sani Mohammed Dambam, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cutar ƙanjamau, tarin fuka da zazzaɓin cizon sauro na jihar Bauchi (BACATMA), a matsayin kwamishinan lafiya da Injiniya Mohammed Andulkadir, kwamishinan kasuwanci da masana’antu, ya maye gurbin Muhammad Baba Maaji, sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar Hukumar Bauchi.

An kuma rantsar da Dr. Ahmed Abdulrahman, mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG) mai ritaya, kuma fitaccen malamin addinin Islama, a matsayin sabon mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro.

Da take jawabi a madadin sabbin kwamishinonin da aka rantsar, Hajiya Babantakko ta gode wa gwamnan bisa amincewar da ya yi musu na naɗin tare da yin alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ciyar da jihar gaba.

By ukarofi