‘Yan ta’adda 152 sun sheƙa lahira, wasu 109 sun shiga hannu – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hedikwatar Tsaron Najeriya DHƙ a ranar Juma’a ta bayyana cewa a cikin makon jiya dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 152, sun kama wasu 109 sannan sun ceto mutum 91 da aka yi garkuwa da su a ƙasar nan.

Kakakin rundunar Edward Buba ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce a cikin wannan makon dakarun sun ragargaza maboyar gwankayen ‘yan bindiga da suka haɗa da Sadiku da maɓoyarsa ke tsaunin Tsora a ƙaramar hukumar Safana jihar Katsina da Alhaji Yusuf da maɓoyarsa ke ɗakin Yadi dake ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

A waɗannan wurare dakarun sun ƙwato AK-47 guda 95, bindigogi ƙirar hannu 35, bindigar mafarauta 76, GPMG daya , PKT biyu da harsasai da dama.

A Arewa maso Gabas Buba ya ce ‘Operation Haɗin Kai’ sun kashe mahara 63, sun kama wasu 38, sun ceto mutum 35 da aka yi garkuwa da su kuma sun ƙwato makamai da dama.

Ya ce daga ranar 28 ga Agusta zuwa 4 ga Satumba mahara tare da iyalen su 196 sun miƙa wuya da a cikinsu akwai maza 19, mata 70 da yara ƙanana 107.

Buba ya ce rundunar sojin sama a ranar 31 ga Agusta sun kashe shugaban ƙungiyar ISWAP Goni Sanda da wasu dakarunsa a jihar Borno.

A Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ‘Whirl Stroke’ sun kashe ‘yan ta’adda uku, sun kama wasu 40 sannan sun ceto mutum 28 da aka yi garkuwa da su.

A Arewa maso Yamma rundunar ‘Operation Hadari sun kashe ‘yan ta’adda 105, sun kama 21, sun ceto 36 da aka yi garkuwa da su sun kuma kwato makamai da dama.

Rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe mahara 16, sun kama 9 sannan sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su.

A Neja-Delta Buba ya ce dakarun ‘Operation Delta Safe’ sun ragargaza matatar mai 58 da aka yi su ba bisa dokar ba, rijiyoyin mai 36, jiragen ruwa 40.

By ukarofi