Farashin mai: Yadda ƙungiyoyin Hausawa, Yarabawa da Igbo suka dunƙule

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A Nijeriya ƙungiyoyi da dama, waɗanda suka haɗa da Afenifere ta Yarabawa zalla da ta ‘yan kabilar Igbo ta Ohanize Ndigbo da ƙungiyar gamayyawar al’ummar Arewa ta CNG, sun yi magana da murya ɗaya cewa ya zama wajibi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo da tallafin mai muddin ana son ƙasar ta ɗore.

Kungiyoyin dai sun ce ‘yan Najeriya sun faɗa halin da ba sa ma iya ciyar da kansu a rana sakamakon tsananin tsadar da ƙarin man fetur ta haddasa.

Wannan ne karon farko da gamayyar ƙungiyoyin suka haɗu wuri guda, kan manufa guda da kuma ta shafi dukkan ƴan Najeriyar.

A cikin sanarwar, mai magana da yawun ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere Jayi Ajayi, ya ce tsare-tsaren da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fito da su, sun jefa ‘yan Nijeriya cikin halin ni-ƴa-su.

Shi ma mai magana da yawun ƙungiyar ‘yan kabilar Igbo ta Ohanize Ndigbo, Mazi Okochuku, ya ce rashin tallafin man fetur ya janyo matakan gwamnatin Tinubu da suka haɗa da bai wa ɗalibai tallafin bashin kuɗin karatu, ya zama tamkar an ba su da hannun dama, an karɓe da hannun hagu.

A nata ɓangaren gamayyar ƙungiyar al’ummar Arewa ta CNG ta bakin shugabanta Jamilu Aliyu Chiranci, ta ce gwamnatin Najeriyar na ɗaukar kukan da ‘yan ƙasar ke yi na matsi tamkar kukan tsuntsaye.

Chiranchi ya ƙara da cewa ”ƙarin kuɗin man fetur bai zo mana da mamaki ba, amma kuma mun yi mamaki saboda mu ne ƙungiyar farko da muka nusar da gwamnati kan yanayin da ƙasa ke ciki, mun samu labarin raɗe-raɗin za a ƙara farashin mai. Mun shaida musu ‘yan Najeriya ba za su iya ɗaukar ƙarin farashin mai ba, saboda halin ƙuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.’’

Ya ƙara da cewa kwanannan a ka yi zanga-zangar tsadar rayuwa da abubuwan da suka faru a lokacin, da ƙoƙarin da aka yin a shawo kan ‘yan Najeriya domin kauce wa kazancewar lamuran da ka iya durƙusar da ƙasar.

Chiranci ya ce abin takaici da kunya shi ne yadda gwamnati ta nuna ‘yan ƙasa ba kukansu ne a gabanta ba.

A makon da ya wuce ne dai aka wayi gari da sanarwar babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL na ƙarin farashin litar mai daga naira 6,17 zuwa naira 8,97 lamarin da ya sake jefa ‘yan ƙasar cikin mawuyacin hali.

Inda ake saida litar man daga naira 1,000 har 1,200 a wasu gidajen mai na ‘yan kasuwa.

Manyan jam’iyyun adawar ƙasar PDP da LP, da ƙungiyoyi da dama ciki har da ta ƙwadago wato NLC sun yi kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sake lale kan wannan mataki sakamakon yadda tuni ‘yan Najeriyar ke cikin mawuyacin hali sakamakon cire tallafin mai da Bola Tinubu ya yi a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki.

By ukarofi