Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi gargaɗi ga malaman makarantun sakandare 250 da aka horar kan su guji yin sakaci kan aikin su, tana mai cewa duk wani malami da aka samu yana da halin rashin ɗa’a da rashin zuwa aiki zai fuskanci hukuncin ladabtarwa bisa ga doka.
Kwamishinan Ilimi, kimiyya da fasaha, Hon. Abdulmalik Gajam ne ya bayar da gargaɗin a yau Asabar a bikin rufe taron horar da malamai na tsawon makonni biyu na shirin Global Standard Change Program (GSTTP) da aka gudanar a Gusau.
Shirin gina ƙarfin aiki ya samu hirar da malaman makarantun sakandare 250, da masu tantance hukumar ingancin Ilimi, da masu kula da ilimi a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Horarwar, an gudanar da ita tare da haɗin gwiwar Noble Hall Limited. Ta mayar da hankali kan hanyoyin koyarwa na zamani, kula da azuzuwa, da kuma tabbatar da inganci don daidaita tsarin ilimin Zamfara daidai da ƙa’idodin Ilimi ta duniya.
Kwamishinan ya ce shirin wani ɓangare ne na dabarun saka hannun jari a cikin mafi mahimmancin albarkatu na kowane tsarin ilimi.
Gajam ya danganta horon kai tsaye da ayyana dokar gaggawa kan Ilimi da gwamna Dauda Lawal ya yi.
A cewarsa, ilimi ya kasance ginshiƙin ajandar gwamnatin Jihar na ceton jihar.
Ya ce ma’aikatar za ta ƙara sa ido kan yadda malamai ke gudanar da aikin su a makarantun Jihar don samun Ilimi nagartacce.
“Duk wani malami da aka samu yana sakaci da ayyukansa za a yi masa hukunci daidai da doka.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta riga ta fara aiwatar da manufofi da nufin inganta walwalar malamai, da kuma gyare-gyaren cibiyoyi Ilimi a faɗin jihar.
Gwamna Dauda Lawal wanda shugaban ma’aikata Alh. Sani Haidara ya wakilta ya sake nanata alƙawarin gwamnatinsa na ci gaba da saka hannun jari a tsarin ilimi.
Gwamna ya yi kira ga waɗanda suka amfana da su isar da ilimi da ƙwarewar da suka samu don ilimantar da ɗaliban su.
“Ina ƙarfafa ku da kuyi amfani da abin da kuka koya a nan don inganta Ilimin ɗalibanmu”. Gwamna Dauda ya ce
