
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas da suka haɗa da na Adamawa, Gombe, Taraba, Yobe, Bauchi da Borno, sun amince da haɗa hannu da Hukumar Kula da Harkokin Almajirai da Ilimin yaran da ba sa zuwa Makaranta (NCAOOSCE) don samar da ofisoshi a kowacce jiha.
An cimma matsayar hakan ne a yayin zaman gwamnonin a Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe, ranar Alhamis.
Haka kuma sun amince da sanya almajirai da yaran a makarantun boko don su shiga sahun sauran yaran da ke zuwa makaranta.
Ƙungiyar gwamnonin za ta yi hakan ne da haɗin-gwiwar NCAOOSCE ta yadda za a kafa ofisoshin da za su riƙa kula da ɓangaren a jihohin.
A sanarwar da ta fitar ta hannun Shugabanta kuma Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ƙungiyar ta kuma koka game da sake farfaɗowar ayyukan ta’addanci a shiyyar, inda ta yi kira ga sojoji da sauran hukumomin tsaro da su samar da tsare-tsaren da za su kawo ƙarshen matsalar a yankin baki ɗaya.
Lamarin da ta ce, sai an daƙile kafin a samu bada ilimi mai nagarta ga ɗalibai a ɓangarori daban-daban da kuma samar da hanyoyin inganta matasa da ƙoƙarin rage talauci acikin al’umma.
