Kwankwasiyya ta amsa amanarta kuwa bayan shekara biyu akan mulki?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

Masu iya magana na cewa, duk inda tafiya ta kai rabi, to a kan tsaya a yi “waiwaye adon tafiya” ba don komai ba sai don yi wa kai hisabi a tantance nasara ko akasi, domin ɗaura ɗamarar ƙarasa tafiya bisa manufa. Gwamnatin Kwankwasiyya ta zo wannan gaɓa a yanzu. Don haka ya kamata mu taya ta wannan hisabi, domin izina wajen ɗaura sabuwar ɗamarar tunkarar zaɓe mai zuwa.

Duk mai bibiyar tarihin siyasar Kano a ’yan shekarun nan ya san irin farin jini da kuma ƙalubalen da ƙungiyar siyasar ta fuskanta a zaɓukan 2019 da 2023. Kowa ya ga yadda suka kama hanyar lashe zaɓe a 2019 kafin a ƙirƙiro ‘inconclusiɓe’ wajen kayar da su. A 2023 an yi iya abinda za a yi, domin sake kayar da su, amma da yake rubutaccen al’amari ne, abin ya gagara. An koma kotu da ƙoƙarin ƙwace zaɓen ta hanyar shari’a, wanda ya haifar da tsaiko a gwamnatin tare da mummunar fargaba ga jagororin tafiyar da mabiya, amma shi ma sai Allah ya yi Allansa yadda Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen Abba Gida-Gida.

To, a sunnar Ubangiji, cewa ya yi, “La’in shakartum la’azidan nakum”. Wato idan Allah ya yi maka ni’ima ka gode, sai ya ƙara maka. Idan kuma ka butulce masa haƙiƙa zai azabtar da kai. Haƙiƙa Allah ya yi wa Kwankwasiyya babbar ni’ima wajen kawar musu da baƙin cikin 2019 ta hanyar faranta musu a 2023. Shin Kwankwasawan sun gode da wannan ni’imar kuwa? Abinda wannan maƙala za ta duba kenan.

Ana nasara a zaɓe sai gwamnatin ta shigo a fusace, sakamakon farko da ta yi wa Kanawa shine na lalata musu dukiya ta hanyar rusau da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin Najeriya, da sunan ‘ramuwar gayya’, yadda a cikin wata guda ta salwantar da dukiyar da aka ƙiyasta ta kai kimanin Naira biliyan 126, kuma wannan ya faru ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya durƙusar da tattalin arzikin Nijeriya sakamakon cire tallafin mai. 

Abu na biyu shine, a cikin wannan mawuyacin halin tattalin arzikin, sai kuma gwamnatin ta ƙaddamar da kataferen aikin gadojin sama a ƙofar ɗan Agundi da Tal’udu, wanda a rahoton jaridar ɓanguard ya ce za su laƙume Naira biliyan 27. Wannan aiki na zuwa ne a lokacin matsanancin halin tattalin arziki da ƙarancin ruwan sha, lalatattun ajijuwan makarantu da miliyoyin matasa marasa aikin yi da suka zaɓi gwamnatin da waɗanda ba su zaɓe ta ba.

Kwatsam, ana tabbatar da hukuncin Kotun ƙoli kuma, kamar matsaloli ba su ishe mu a Kano ba, sai ga dokar dawo da Sarki Muhammadu Sanusi kan karagar Sarkin Kano, lamarin da ya jefa jihar a ruɗanin siyasa da ba a taɓa ganin irinsa ba. Shin Kanawa sun cancanci gwamnatin da suka zaɓa ta ci gaba da haifar musu da koma-baya haka? Shin su sarakunan biyu sun yi wa gidan sarautar da mutanen Kano adalci wajen nuna irin wannan haɗama, wacce ta rushe duk wata ƙima da gidan mai tarihin shekaru sama da dubu ya ginu a kanta?

Duk da mu ’yan jarida ne ba ’yan siyasa ba, amma babban aikinmu shine goyon bayan mulki na adalci da yaƙar na zalunci ba tare da la’akari da siyasa ba. Wannan dalili ya sa mu ka yi ta jan hankali a zaɓi Buhari da APC sakamakon zaluncin da Arewa ta fuskanta a hannun PDP da Jonathan a 2015. Daga baya mun koma sukar Buhari da APC bayan zangon farko (2015-2019) yayin da suka gaza yin adalci, muka ci gaba da nuna a sami canji a 2023. Matuƙar masu zaɓe za su riƙa amfani da damarsu wajen ko da aƙalla korar duk wanda suka zaɓa bayan shekara huɗu, saboda ya gaza kawo canji rayuwarsu, to wataƙila hakan ya sa wanda duk aka zaɓa ya tsaya ya yi wa mutane aiki.

A shekaru biyu na mulkin Kwankwasiyya, ba a taɓa samun gwamnatin da ta sami kuɗaɗe daga Asusun Tarayya ba irin ta, amma me rayuwar Kanawa ta mora? Haƙiƙa akwai waɗancan gadojin sama da muka ambata, kuma ana ta gyara titina a cikin birni tare da ƙawata su da fitilu masu amfani da hasken rana gwanin sha’awa. Amma magana ta gaskiya, shin wannan kaɗai talakawa ke buƙata..? A jihar da ruwan sha ke neman gagarar mutane..? Abinci ya yi tsadar da mutane da dama ba su iya ci sai uku?

A wannan makon kuma sai ga gwamnati ta bijiro da aikin rushewa da sake ginin Majalisar Dokoki ta Jihar Kano akan kuɗaɗen da ake hasashe kimanin Naira biliyan 40. Gabaɗayan ’yan majalisar Kano su 40 ne, da ma’aikata waɗanda ba su wuce 200 ba, duk da cewa ginin majalisar tun Abubakar Rimi aka fara gina shi, don Allah a wannan mawuyacin halin tattalin arziki da jama’a ke ciki shine abin da Kanawa ke buƙata?

Me ku ke tsammani maimakon kashe wannan uban kuɗi har Naira biliyan 40, a ce an saka shi a fannin noma ko samar da ayyukan yi da jari ga matasa, ko a harkar lafiya ko sufuri? Me ku ke tsammani da gwamnatin ta bi shawarar da a tsawon shekaru biyun nan nake ta ba ta kan yadda za ta raya da amfanar da, ba Jihar Kano kaɗai ba har maƙwabta, wajen tashin dama-damanmu daga barci?

Tun shigowar wannan gwamnati, babu wanda ya saka ni, na ɓata lokacina na yi nazarin kasuwanci (feasibility studies) akan yadda za a amfani da dama-damai 22 da muke da su, amma suna barci tsawon shekaru 40. A ɓangaren noman kifi kawai, Najeriya na siyo kifi na Dala biliyan 2.3 a shekara daga waje. Hatta ƙasar Mauritania da ke yankin sahara na siyar mana da kifi na Dala miliyan 50 (Biliyan 75), amma Kano na da dam guda 22 su na barci?

A wancan binciken da na yi har wani babban kamfani a Chana na tuntuɓa kuma suka nuna sha’awar za su zo su saka jari. Abinda kawai su ke so shine a gayyato su su zauna da Gwamnatin Jihar Kano su yi yarjejeniya. Na zauna gaba-da-gaba da kwamishinoni guda biyu da kuma Sakataren Gwamnati, sannan na tura wa gwamna ‘proposal’ (wadda ban sani ba ko ya gani), domin su ɗabbaƙa wannan shiri, amma an yi biris da maganar.

Idan gwamnati ce za ta sa a yi wannan ‘feasibility studies’, sai ta biya ‘consultants’ miliyoyin Naira, amma su na zaune na je na yi aikin kuma babu wanda na ce ya ba ni sisin kwabo, kuma ba ni za a bawa wannan kwangilar ba, amma Ina ta bibiyar su da ba su damar da za su zarta kowa wajen tara kuɗaɗen shiga ta hanyar amfanar dama-damanmu, amma kamar hakan ba shine a gabansu ba, ko? Duk wanda ka yi magana da shi rimi-rimi, sai ya daina ɗaukar waya? Yayin da ’yan Chana har shaguɓe su ke yi min, saboda sun gaji da kira na su na son jin yaushe za su zo a fara tattaunawa?

Ta wannan hanyar ta noman kifi kawai a waɗannan dam, wallahi Kano za ta iya karkato wa kanta kuɗaɗen shiga na tiriliyan ɗaya ko fiye da haka a duk shekara cikin tiriliyan 3.4 da ake kwasa zuwa waje, don siyo kifi a Nijeriya.

Kano ta shiga mawuyacin halin rashin ruwa da aka daɗe ba a ga irinsa ba, amma a wata ukun farko na shekarar nan (2025), Naira miliyan 245 kacal aka saka a harkar ruwan sha. Amma kuɗaɗen da aka kashe wajen kwasar girki da taɓa-ka-lashe na manyan jami’an gwamnati a wannan tsuku Naira miliyan 247 ne. Sannan an kashe Naira biliyan 1.1 wajen kara-kainar mahukunta a jiragen sama a cikin gida da ƙasashen waje, banda ware wata Naira biliyan 1.1, don saka wutar sola a gidan gwamnati.

Ko kun san cewa dam guda biyu cikin 22, wato na Tiga da na Challawa, suna da ruwa ‘cubic litre’ sama da biliyan uku? Wannan ruwa na dama-daman nan guda biyu zai iya shayar da mutane biliyan uku ruwa na tsawon shekara guda a lita dubu kowane mutum a shekara (wato Kano za ta iya shayar da Afirka gabaɗaya da wasu ƙasashen na tsawon shekara, amma dama-daman su na sharɓar barci?). Kuma tun aikin matatar ruwa na Tamburawa a lokacin Malam Ibrahim Shekarau, ba a sake samun wani babban aiki, domin samar da ruwa a Kano ba. Kuma a duk wata ana haihuwar sabbin jarirai 27,000 a Kano? Me ake yi wa masu tasowa tanadi ne?

Irin wannan halin ko-in-kula na shugabanni da saka buƙatunsu sama da na talaka a Kano shi ya janyo mana abin kunya, wato muka rasa jagoranci na shekaru sama da 100 wajen tara kuɗaɗen shiga.

A shekaru biyun nan Kano ta karɓi kuɗaɗe daga tarayya a 2023 har Naira biliyan 178, sannan a 2024 ta karɓi Naira biliyan 200, jumlatan Naira biliyan 379. Amma babu wani abu ƙwaya ɗaya da aka assasa wanda zai haɓaka kuɗaɗen shiga na jihar. Kashi 90 na kuɗaɗen na tafiya akan ma’aikatan gwamnati, ’yan siyasa da ayyukan ƙyale-ƙyalen gari kawai.

Wannan dalili ya sa aka wayi gari Jihar Kaduna ta zarce mu, sakamakon karkata hankulansu wajen jawo masu saka jari. Gwamnoninmu sun fi mayar da hankali wajen kashe kuɗaɗenmu yadda su ke so ba yadda muke buƙata ba, wajen gina gadojin sama kawai ko wasu gine-gine.

Haka nan mu na gani yadda Gwamnan Jihar Jigawa, Malam ɗan-Moɗi, a kullum ya na ta haƙilon jawo masu saka jari a jiharsa, musamman a harkokin noma, kuma nan gaba kaɗan Jigawa ma na iya zarta mu a hanyoyin kuɗaɗen shiga idan aka tafi a yadda ake.

Mun yaƙi gwamnatin Ganduje da tsammanin Kwankwasawa za su kawo canji ga talaka, amma sai abin ya ke neman zama sammakal ko ma gara jiya akan yau. Kamar yadda na faɗa a baya, mu ’yan jarida ne ba ’yan siyasa ba, don haka ba kwangila muke nema ba, illa dai mu nusar da gwamnati zuwa duk wani abu da zai zama alheri ga talaka kuma masu mulki su tsira gaban Allah.

Sannan akwai tulin ’yan siyasa da suka tallafa wajen zaɓar gwamnatin nan, amma an yi watsi da su an janyo ’yan bani-na-iya. Kowa ya san ba wanda ya yi jihadin karɓar mulki a wannan karo irin tsohon Sakataren Gwamnati, kuma duk da an yi masa sakayya da muƙami, to kuskure ne babba a bar shi ya zama maƙiyi, domin akwai illa a hakan. 

Yanzu dai saura shekara ɗaya ta aiki, kuma a halin da ake ciki na san Kanawa da dama ba su gamsu da kamun ludayin wannan gwamnati ba, musamman wajen ayyuka da a haƙiƙa mutanen Kano ke buƙata. An zargi gwamnatin da ta shuɗe da amfani da kuɗin takalmi na kaso 15-25 wajen bayar da kwangila, shin ko shi ya sa a yanzu ma aka fi mayar da hankali akan ayyuka irin na gadojin da ginin majalisa? 

A ƙarshe Ina son gwamna ya tuna lokacin da matar wani babban jami’i ta ci mutuncinsa a filin jirgin sama, saboda ta na taƙamar su ne da mulki a lokacin, yau tana ina..? Shi kuma ya na ina? Haka tsarin duniya yake, yau gare ka, gobe ga waninka. Don haka mahukunta su san da cewa akwai ranakun jin kunya guda biyu matuƙar ka karɓi amana, amma ka kasa cika ta: Ta farko a nan duniya, wato ranar da ka faɗi zaɓe ko ka gama wa’adinka, sai kuma a lahira gaban Allah.

Kusan kowa na yabon halayen kirkin gwamna kuma ba mu manta yadda a lokacin mulkin Dawo-Dawo, irin yadda a ƙarƙashin kulawarsa ya na kwamishinan ayyuka, kowane sashe na gwamnati ya haɓaka. To, yaya ga wuƙa da nama a hannunsa yake neman gazawa kuma lokaci ya taso ƙurewa? Babban dalilin bai rasa nasaba da kewaye kansa da mutane da aljihunsu kawai, ba jama’a ne a gabansu ba.

Don haka Kwankwasiyya ku farka, domin a rabin zango tafiya, takardar shaidarku ba ta kai ‘pass-mark’ ba… amma ku na da damar samun cikakkiyar nasara idan kun sauke AMANA da kuka ɗauka, idan dai ba cewa tambarin AMANAR taku dama a baki kawai ta tsaya ba. 

Allah ya ba ku iko!

Malam Sadiƙ manazarci ne daga Jihar Kano

By ukarofi