Shugaban NANS ya zargi Seyi Tinubu da sa ƴan daba su yi masa duka bisa ƙin karɓar cin hancin miliyan N100

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), Atiku Abubakar Isah, ya zargi ɗan Shugaba Bola Tinubu, wato Seyi Tinubu da aika wasu ƴan daba su yi masa dukan kawo-wuƙa saboda ya ƙi amincewa da karɓar cin-hancin Naira miliyan 100.

Isah, wanda aka zaɓe shi a yayin taron ƙungiyar da aka yi a ranar 27 ga watan Fabrairu, ya yi zargin cewa Seyi ya zo wajen rantsar da shi a Abuja, ranar Talata, inda ya yi ƙoƙarin hargitsa wajen tare da yi wa rayuwarsa barazana.

Ya kuma ce, ɗan shugaban ƙasar ya je otal ɗin da aka yi taron ne da wasu gungun jami’an tsaro tare da umartar su da su dakatar da taron.

Ya ƙara da cewa, hukumar gudanarwar otal ɗin sai da ta gargaɗe shi game da tsaiko da ka iya bijirowa, amma duk da haka ya ce a cigaba da taron.

Bayan Sanata Ibrahim Shekarau ya fara jawabi ne sai jami’an suka kutso cikin ɗakin taron ɗauke da bindigu da adduna, inda suka dakatar da Sanatan tare da fara saran mutane da ƙwace wayoyin hannu da wasu kadarori daga gare su.

A nasa ɓangaren, Seyi Tinubu ya ƙaryata zargin da Kwamared Atiku Abubakar Isah ya yi akansa na yin barazana ga rayuwarsa, kamar yadda ya wallafa ta kafar Instagram.

A ranar Talata ne Seyi ya bayyana zargin a matsayin abinda da aka ƙirƙira da zimmar ɓata masa suna, ya na mai cewa labarin ba gaskiya bane.

By Babaji