A wani rahoto da RFI ta fitar ta ce, sama da ƴan-ci-rani 72,000 sun mutu, wasu kuma sun yi ɓata-dabo a ƙoƙarinsu na tsallakawa zuwa ƙasashen Turai tun daga shekarar 2014, kamar yadda alƙaluman Majalisar ɗinkin Duniya suka nuna.
Hukumar Kula da Ƴan-ci-rani ta Duniya ta ce, an fi samun asarar rayukan ƴan-ci-ranin a bara, inda adadinsu ya kai 8,938, a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasashen Turai da zummar samun ingantacciyar rayuwa.
Hukumar ta bayyana adadin a matsayin mai tayar da hankali wanda kuma ke nuni da irin kasadar da jama’a ke ɗauka da zarar sun rasa tsaro da damammaki a ƙasashensu na asali.
Rahoton ya ce, kashi ɗaya bisa uku na ƴan-ci-ranin da suka mutu ko suka ɓace sun gamu da rashin tsaro da rikce-rikice da rashin agaji, abin da ya tilasta musu ficewa daga ƙasashensu.
Mutun ɗaya cikin huɗu na ƴan-ci-ranin sun fito ne daga ƙasashen da ke fama da rikici, kuma dubbai daga cikinsu ƴan Afghanistan da Rohingya da Syria ne .
Har ila yau, rahoton ya ce, sama da mutum 52,000 sun mutu a ƙoƙarinsu na tserewa daga ƙasashen duniya 40 da Majalisar ɗinkin Duniya ke bai wa tallafi.
Har yanzu dai, babu hanyar da ta fi zama siraɗin mutuwa ga ƴan-ci-ranin kamar tekun Mediterranean, inda a wannan hanyar kaɗai, aka samu asarar rayukan ƴan-ci-ranin dubu 25 a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Kazalika akwai sama da ƴan-ci-ranin 12,000 da suka ɓace a tekun bayan sun tsere daga ƙasar Libya da yaƙi ya ɗaiɗaita, baya ga wani adadi mai tarin yawa da suka ɓace a yayin tsallakawa ta Sahara
