
Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da ake dakon fitar da sakamakon bincike na rahoton zargin Shugaba Bola Tinubu da ta’ammali da ƙwayoyi a shekarun 1990s, Cibiyar Bincike da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, wato FBI da DEA a Amurka, sun bayyana wa reshen Kotun Shiyya ta ƙasar Colombia dake Amurka cewa suna buƙatar a ƙara masu watanni uku domin kammala haɗa takardun rahoton.
Hukumomi biyun sun bayyana hakan ne a wani saƙon haɗaka zuwa ga kotun tare da wanda ya shigar da ƙarar, wato Aaron Greenspan.
Saidai, Greenspan ya ƙi amincewa da buƙatar, inda a madadin haka ya zaɓi a ba su makonni biyu don fitar da takardun.
Da farko dai Kotun ta umarci hukumomin da su kammala tare da fitar da rahoton a ranar 2 ga watan Mayu, 2025, duba da kula da ƴancin sanar da al’umma ta kundin dokar ƙasar.
Tun a tsakanin shekarun 2022 da 2023 ne Greenspan ya shigar da ƙararraki 12 na FOIA kan fitar da rahotonnin ta’ammali da ƙwayoyi na ‘Chicago drug ring’ da aka yi a farkon shekarun 1990s.
Daga cikin buƙatun da ya gabatar akwai waɗanda suke da alaƙa da Shugaba Tinubu da wasu mutane uku da suka haɗa da Lee Andrews Edwards, Mueez Adeboyega Akande da Abiodun Agbele.
