
Ƙungiyar gwamnonin Arewa (NGF) ta sake nanata buƙatar kafa ƴan sandan jihohi domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Cikin sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan kammala taron da ta gudanar a Kaduna, gwamnonin sun yi kira ga majalisar dokokin Nijeriya da na jihohi su ɗauki matakan tabbatar da hakan.
Matakin gwamnonin na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ƴan sanda domin magance matsalolin tsaron da sassan ƙasar ke fuskanta.
Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar a makon da ya gabata ya ce zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƴan sandan jihohin.
NGF ta kuma miƙa saƙon jajentawa ga gwamnatoci da al’ummar jihohi da dama bisa munanan hare-haren ƴan ta’adda ciki har da Kebbi, Kwara, Kogi, Niger, Sokoto, Jigawa, da Kano, inda aka yi awon-gaba da ɗalibai da wasu jama’ar gari.
Haka kuma, ta jajenta wa waɗanda musibar Boko Haram ta shafe su a jihohin Borno da Yobe.
Kazalika, ta ci alwashin ba sojoji cikakken goyon baya a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa acikin al’umma.
