Shugaban ƙasa, mun yi murna da dokar ta-ɓaci

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Babu shakka sanarwar da fadar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fitar a ranar Laraba, 26 ga Nuwamba 2025, game da ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban ƙasar ya yi, a duk fadin ƙasar kan harkokin tsaro saboda ƙaruwar masu garkawa da mutane da kai hari kan ’yan makaranta, da wuraren ibada, a wasu jihohin Arewa kamar su Kebbi, Neja, da Kwara, abin farinciki ne sosai, kuma abin a yaba ƙwarai da gaske. Lura da halin da ƙasar ta shiga na ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro, daga yankin Arewa Maso Yamma, da Arewa Maso Gabas, da kuma yankin Arewa ta Tsakiya. Wannan mataki zai ƙara wa jami’an tsaron mu ƙwarin gwiwa, kuma zai ba da damar fitar da ƙarin kuɗaɗe, domin sayen kayan aiki da jami’an ke buƙata, har da batun albashi da alawus ɗin sabbin jami’an da za a ɗauka.

Daga cikin saƙon shugaban ƙasar da aka fitar akwai batutuwan da aka yi bayanin su ƙarara, kamar cewa da aka yi, rundunar ‘yan sandan Nijeriya za ta ɗauki ƙarin jami’ai 20,000, wanda zai mayar da adadin ‘yan sandan da ake da su zuwa 50,000, tare da mayar da sansanonin masu hidimar ƙasa (NYSC) wurin horo na gaggawa. Sannan ya umarci rundunar tsaro ta farin kaya, wato DSS ta aika da sabbin jami’an da aka horar kan aikin tsaron daji, domin kawar da ‘yan ta’adda daga cikin dajin, tare da ƙarfafa ƙoƙarin sojoji a yankunan da ke cikin haɗari. Ya kuma buƙaci Majalisar Dokokin Tarayya ta fara aiki kan dokar samar da ‘yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro a matakin jihohi.

Wannan sabon umarni na shugaban ƙasa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar nan, wanda ke gajiyar da jami’an tsaron da ake da su a ƙasar nan. Lura da irin ɗimbin ayyukan dake gaban su na samar da tsaro da zaman lafiya a wuraren da ake samun ƙalubalen tsaro a ɓangaren Kudu da Arewa bakiɗaya. Kafin fitar da wannan sanarwa ta baya bayan nan, mun ji wani umarnin da Shugaban ƙasa ya fitar bayan ganawarsa da shugabannin rundunonin tsaro, inda ya memi a janye dukkan jami’an ’yan sandan dake bai wa manyan ’yan siyasa da masu faɗa a ji kariya, domin ƙara adadin jami’an dake gudanar da aikin tsaro. Kuma ko a sabon umarnin da aka fitar Shugaban ƙasa ya nemi a tura waɗannan jami’an zuwa samun ƙarin horo na musamman da zai ƙara gogar da su don tunkarar ƙalubalen da ke gabansu.

Babu shakka wannan yana daɗa nuna mana irin jajircewa da tashi tsayen da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi na ganin an yi duk mai yiwuwa, domin ceto ƙasar nan daga hannun ’yan ta’adda dake neman yi wa ƙasar ƙawanya, da ƙwace iko da sassan ƙasar nan. Idan ba mu manta ba, shugaban ya dakatar da tafiye-tafiyen da ya kamata ya yi don wakiltar Nijeriya a wasu manyan taruka na duniya, kamar taron G20 da aka gudanar a ƙasar Afirka ta Kudu a makon da ya gabata. Sannan a kowacce rana cikin tattaunawa da tuntuɓa yake, don ganin ba a samu wani cikas a ƙoƙarin da ake yi ba, yayin da jami’an tsaro ke cigaba da ba da haɗin kai wajen amfani da dabaru daban-daban, don sauke nauyin dake kansu.

Kodayake ’yan Nijeriya suna ta bayyana mabambantan ra’ayoyi game da batun, sai dai ra’ayi mafi rinjaye ya karkata ne kan yabawa matakin na shugaban ƙasa da ƙoƙarin da yake yi na inganta aikin jami’an tsaro, don iya tunkarar ƙalubalen da ake ciki. Wasu masu nazari kan harkokin tsaro irin su Bulama Bukarti, Ahmad Sajoh, da Ajayi Okasanmi sun buƙaci ɗaukar matakai na zahiri da yin aiki da umarnin da aka bayar domin dawo da ƙwarin gwiwa da yardar ‘yan ƙasa akan gwamnati. Sun goyi bayan Majalisar ƙasa na ƙin amincewa da biyan kuɗin fansa ga ‘yan ta’adda, don karɓo waɗanda suka sace, domin a cewarsu hakan na ƙara wa ’yan ta’adda ƙwarin gwiwa ne, da kuma ba su damar ƙaro makaman da za su yaƙi gwamnati. 

Wannan ra’ayi nima a kansa nake! Wajibi ne ne a nuna wa ’yan ta’adda cewa lallai gwamnati ba abin wasa da rainawa ba ce. Kuma bin ɗan ta’adda ta hanyar lalama da sasanci yana ƙara bashi ƙwarin gwiwa ne, har ya riƙa ganin kamar ƙarfin sa da isar sa ce tasa ake bin sa a hankali. Lallai ne gwamnati ta nuna da gaske take yi, a nuna musu babu sani babu sabo. Duk wanda ya ɗauki makami akan ‘yan Nijeriya a ko’ina suke, ya kuma ƙalubalanci ikon gwamnati da jami’anta, lallai a nuna masa iyakarsa. Kada a nuna masa tausayawa, kamar yadda ba ya nuna tausayawa ga waɗanda yake kamawa ko yake yi wa kisan gilla.

Abin farinciki ne yadda gwamnati ta amsa kiraye-kirayen da ake yi na samar da rundunar tsaro ta musamman da za ta kula da batun tsaro a dazukan ƙasar nan, da nufin kakkaɓe ɓata-gari da ke kafa sansanoni a cikin dazuka suna shirya hare-haren ta’addanci akan ‘yan Nijeriya. Mun ji daga Shugaban ƙasa cewa, jami’an ‘yan sandan farin kaya da aka yi wa horo na musamman za su bazama cikin dazuka domin farautar ’yan ta’adda. Wannan ma abin yabawa ne ƙwarai da gaske.

Ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar shigar da masu aikin hidimar ƙasa da ’yan banga da suke samun horo kan aikin tsaro a cikin unguwa unguwanni da ƙauyuka da cikin dazuka su ma a shigar da su cikin sabbin jami’an tsaron da za a ɗauka, wazanda ba sa buƙatar horarwa mai yawa, kuma za su iya shiga cikin dazuka da sauran abokan aikinsu, don cigaba da aikin da suka saba. Abin da gwamnati take buƙata shi ne ba da umarni, cire siyasa da son zuciya wajen ɗaukar jami’an tsaro, cire ɓata-gari masu kawo cikas ta hanyar neman na goro kafin a ɗauki mutumin da ya cancanta cikin aikin tsaro. Sannan a samar da ingantaccen tsarin da zai tabbatar da ba a yi kitso da ƙwarƙwata ba, wajen shigar da ɓata-gari cikin ɗaukar aikin da za a yi, don a kaucewa samun ƙafar angulu a aikin kakkaɓe ’yan ta’adda. 

Game da batun samar da dokar da za ta bai wa jihohi damar ɗaukar ’yan sandan jihohi da Shugaban ƙasa ya bai wa Majalisar ƙasa damar dubawa kuwa, lallai a tsaya a kafa dokar da ba za ta bai wa gwamnoni damar cin karensu babu babbaka ba. A tabbatar da cewa, an shimfiɗa dokoki da sharuɗɗan da za su hanawa jihohi nuna wariya da fifiko wajen ɗaukar jami’an da za su yi aikin, kuma a ga cewa ba a yi amfani da su ba wajen zama karnukan farauta, don murƙushe abokan adawa ko tsirarun ƙabilu a jihohin da ake samun ƙalubalen tsaro na zamantakewa.

By ukarofi