
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci baki ɗaya jami’an gwamnatinsa da ya naɗa a muƙamai daban-daban da su bayyana kadarorin da suka mallaka.
Gwmanan ya bayyana hakan ne a yayin buɗe-baki da jagororin ma’aikata da masu ba shi shawara na musamman a Gidan Gwamnatin jihar.
Ya ce, kaso 60 zuwa 70 na muƙarraban nasa ba su kiyaye abinda doka ta shar’anta masu ba, ya na mai kira a gare su da su bai wa doka haɗin kai wajen gaggauta bada duk wata takarda da aka buƙaci su kawo.
Haka kuma ya shawarci mashawartansa da su riƙa samar da rahotannin harkokin gwamnati da bibiyar ayyukan da ta ke yi wajen ba ta shawarwarin da suka dace.
Gwamna Abba ya kuma ce an bada kujerun aikin hajji 13 ga jagororin hukumomin gwamnati a jihar.
A nasa jawabin, Sakataren gwamantin, Malam Umar Ibrahim ya tunatar da jami’an game da alƙawarin da suka ɗauka a lokacin da aka rantsar da su, ya na mai kira a gare su da su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da adalci a yayin da gwamnan ke ƙoƙarin inganta rayukan al’ummar jihar.
