Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar dattawa a ranar Talata ta soke matakin da ta ɗauka kan sashe na 28 na kundin dokar zaɓe, inda ta rage yawan kwanakin da INEC za ta sanar da gudanar da zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180.
Sannan ta yi kiran sashen da ya tilasta wa INEC sanar da shirin gudanar zaɓe kafin kwana 300 daga ranar da za ta fitar da jadawalin zaɓe.
Majalisar ta ce, wannan mataki ya zama wajibi bayan da gano kuskure a cikin sashe na 22 na ƙudurin da ya haɗa da sashe na 60 wanda ya yi bayanin cewa ba wajibi ba ne tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet.
Ta hanyar wannan sabon tsari, za a iya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa a cikin watan Disambar 2026 ko watan Janairun 2027.
Wannan mataki ya samu goyon bayan mafi yawan sanatoci ta hanyar tura saƙon murya wanda shi ne ya tabbatar da sake gyaran sassan.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce, shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ya sanar da ranar 20 ga watan Fabarairun 2027 a matsayin ranar zaɓen shugaban zaɓe da na ‘yan majalisa.
La’akari da wannan sanarwa, ranakun zaɓen sun faɗo cikin watan azumin 2027. Kuma tun bayan lokacin ne ƙungiyoyin Musulmai suka riƙa ƙorafi kan sake ranar yin zaɓe domin kaucewa lokacin azumin.
A yayin zaman majalisar, ‘yan majalisar sun sake gyara dokar zaɓen ne domin ƙarfafa wa INEC ta iya sake sauya lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya na 2027 da zummar gujewa yin zaɓukan a watan Ramadan.
Shugaban masu rinjeye na majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudurin.
Mista Bamidele, wanda ke wakiltar Ekiti ta tsakiya, ya ce, gudanar da zaɓen a lokacin Ramadan zai iya shafar yawan mutanen da za su fito zaɓe da shafar zirga-zirga da ba da gudunmowar masu ruwa da tsaki da ɗaukacin sahihancin zaɓen bakiɗaya.
Ya ce, bayan nazari sosai na ƙudurin, akwai bambance-bambance a cikin sassa 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93 da 143 da suka shafi rashin daidaito na wasu al’amuran zaɓe.
Tuntuɓar masu ruwa da tsaki da INEC ta yi:
Mista Bamidele ya ƙara da cewa INEC ta tuntuɓi wasu ‘yan majalisa biyo bayan ƙorafi da masu ruwa da tsaki daga Musulmai suka yi kan neman a sauya ranar gudanar da zaɓe sakamakon azumin watan Ramadan.
Ya ce INEC ta nemi a yi gyaran dokar zaɓe ta yadda zai ba ta damar ta iya yin gyaran jadawalin ranar yin zaɓe.
ɗan majalisa mai wakiltar Filato ta Kudu, Simon Lalong, wanda ke jagorantar kwamitin harkokin zaɓe ya mara wa ƙudurin baya.
Mista Lalong, wanda ɗan APC ne kuma tsohon gwamnan jihar Filato, ya ce, ‘yan majalisar sun shafe shekara biyu suna aiki a kan ƙudurin gyaran dokar zaɓe.
Ya ƙara da cewa jadawalin gudanar da zaɓen da INEC ta sanar ya shafi wani kundi na da shugaban hukumar ya bayar wanda ya shafi harkokin zaɓen tun daga shekarar 2019 zuwa 2031.
Sanatan nya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi wa shugaban INEC adalci suna masu cewa doka ta ba da damar a yi gyara a inda aka ga dacewar hakan.
Shugaban majalisar dattawa daga nan ya ba da dama domin kaɗa ƙuri’a kuma da yawan ‘yan majalisar sun amince da hakan.
