
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa haɗin kai shi ne kaɗai zai taimaka wa samun nasara a ƙasa, ya na mai kira ga shugabannin Nijeriya da su ɗauki darasi daga haɗewar rafin Neja da Benue a yankin Lokoja na Jihar Kogi.
Shugaba Tinubu, wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi a taron taya murna ga Gwamna Usman Dodo na cika shekara ɗaya a mulki, ya ce haɗewar rafukan ba ga iya taswira ta tsaya ba, hakan na nuna ƙarfi a lokacin da aka samu haɗin kai a tsakanin al’ummomi daban-daban don cimma kyawawan manufofi da dama.
Shugaban ƙasar ya yaba wa Gwamna Ododo wajen buɗe ƙofar tattaunawa inda ya bayyana hakan a matsayin wata hikima da za ta taimaka wajen inganta harkokin sulhu da kuma ci-gaba.
Ya kuma yi kira ga jagorori a kowane mataki da su gina gadoji a faɗin ƙasar tare da fifita tattaunawa a matsayin abin warware matsalolin banbance-banbance da ƙarfafa haɗin kai acikin al’umma.

A wata sanarwa da Babban Mai taimaka masa kan harkokin Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar, Tinubu ya yi kira ga al’ummar Kogi da su ɗauki kawunansu a matsayin jinshiƙan samar da ci-gaba ta gudunmawa da za su riƙa bayarwa a matakai da dama.
Da ya ke jawabi, Gwamna Ododo ya yi godiya ga Shugaba Tinubu da al’ummar jihar bisa tallafa wa gwamnatinsa tun farkon hawansa mulki, ya na mai kira a gare su da cigaba da ƙoƙari wajen gina jihar da ci-gabanta ta hanyar amfani da damammakin da take da su.
Ya kuma jinjina wa Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima kan gudunmawarsa tun daga farkon kafa gwamnatinsa shekara guda da ya gabata.
