An shiga halin rashin tabbas yayin da Nijar, Burkina Faso da Mali ke fita daga ECOWAS ranar Laraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne za’a tabbatar da ficewar ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga cikin Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) bayan shekara guda da aka ɗauka na fargabar harkokin siyasar da ta haifar da rashin tabbas ga tafiyar da harkokinta a nan gaba.

A ranar 29 ga watan Junairun 2024 ne ƙasashe ukun, waɗanda sojoji ke mulkar su, suka bayyana matsayarsu ta ficewa daga ƙungiyar. Sai dai abinda dokar ECOWAS ta bada dama game da irin halin shi ne a samu tsawon shekara ɗaya ta sanarwa kafin tabbatar da matsaya.

Lamarin zai fara aiki ne a ranar Laraba, kasancewar ƙasashen, waɗanda suka haɗe kai waje ɗaya, sun yi buris da kiraye-kiyaren ECOWAS na su ƙara watanni shida ko za a sulhunta da su.

A halin yanzu dai Burkina Faso da Mali da Nijar sun haɗe waje guda inda suka samar da ƙungiya mai suna Alliance of Sahel States (AES), wato haɗakar ƙasashen Sahel.

Shugabannin mulkin sojin ƙasashen sun zargi ECOWAS da haramta jagorancinsu bayan juyin mulkin da suka kai su ga zama shugabannin ƙasashen.

Akan haka ne Paris ta ƙasar Faransa ta zama abokiyar gabarsu, waɗanda a yanzu suke ƙawance da ƙasashen Rasha, Turkiyya da Iran.

Lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yulin 2023 wanda ECOWAS ta yi ƙoƙarin dawo da shugaban da aka hamɓarar ta hanyar sanya wa Niamey takunkumin tattalin arziƙi duk da cewa a yanzu an dakatar da shi.

A ranar Laraba ne dai ƙasashen za su fara amfani da fasfo ɗinsu na bai-ɗaya.

Sun kuma sanar da cewa za su ware dakarun haɗaka guda 5,000 don yaƙar masu ikirarin jihadi nan ba da jimawa ba.

By Babaji