
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamishinan ƴan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun kama wani da ake zargi da kuma ƙwato wasu ababen fashewa, biyo bayan sanarwar mummunan hari da ka iya shafar al’ummar jihar.
A yayin taron manema labarai, Kwamishinan ya zayyano matakan da ƴan sanda suka ɗauka don tabbatar da zaman lafiyar al’umma da kuma ba su kariya daga hare-hare.
A ƴan kwanakin nan ne ƴan sandan suka fitar da sanarwar yiwuwar samun mummunan hari a lokacin gudanar da Maulidin Tijjaniyya da ya gabata a jihar da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan al’amarin.
Ya ce jin haka ke da wuya, sai wasu daga cikin waɗanda ake zargi suka riƙa tserewa inda ƴan sanda suka samu nasarar kamo ɗaya daga ciki da ya taho daga wata coci bayan bin diddiginsa.
Kwamishinan ya nuna muhimmancin bayanan sirri wajen daƙile abubuwan da ka iya zama barazana ga al’umma, ya na mai bayyana yadda ƴan sanda suka haɗe kai da masu-ruwa-da-tsaki wajen inganta harkar tsaro a lokacin.
Kazalika, ya yi tsokaci game da aiki a yankin da ke da ƙarfin harkokin siyasa a lokacin da aka yi ƙoƙarin siyasantar da al’amarin, amma kuma ya bada tabbacin ƙoƙarin ƴan sanda na cigaba da kiyaye doka da oda.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da kasancewa masu lura tare da ruwaito duk wani abin zargi da suka gani a yankunansu ga hukumomin tsaro.
