Haɗin kan Musulmi ne maganin matsalolin Arewa, inji Sanata Goje

Spread the love

Daga HABU DAN SARKI a Jos

Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar ƙasa, Muhammad ɗanjuma Goje, ya buƙaci al’ummar Musulmi su haɗa kansu, kuma su yi aiki tare don gina Arewa, da shawo kan matsalolin da suka dabaibaye yankin bakiɗaya. 

Sanatan ya bayyana haka ne a yayin rufe Gasar Musabaƙar Alƙur’ani Mai Girma ta Jihar Filato, karo na 39,wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Babban Masallacin Jumma’a na Jos. 

A ta bakin wakilinsa, Ibrahim Abdullahi Tumu, Sanata Goje ya aika da saƙon zaman lafiya da haɗin kan ‘yan Nijeriya, musamman al’ummar yankin Arewa, inda aka fi fuskantar ƙalubalen tsaro, talauci da rashin ayyukan yi, abubuwan da ke ƙara mayar da yankin baya.

A cewarsa, ba za a samu nasarar kawar da ƙalubalen da ake fuskanta ba tare da haɗin kai da aiki tare tsakanin ýan Arewa da ke kowanne matakin rayuwa ba. 

Babban Baƙo mai jawabi, Dakta ɗanjuma Usman Gwani, na Sashin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci da Larabci a Jami’ar Tarayya da ke Kashere, ya ja hankalin Musulmi da su yi riƙo da koyarwar addinin Musulunci a kowanne al’amari na rayuwa. Tare da cewa, biyayya ga koyarwar Alƙur’ani waraka daga kowacce irin matsala. 

“A matsayin mu na Musulmi, Alƙur’ani ba kawai abin karantawa da tilawa ba ne, ana buƙatar a yi aiki da shi ne a matsayinsa na shiriya kuma haske ga al’umma.”

Dr Gwani ya ƙara da cewa, idan muka yi aiki da karantarwar Alƙur’ani mai girma sau da ƙafa, za mu samu nasarar samun sauƙin damuwoyin da suke addabar ƙasar nan, irin su sace-sacen mutane ana garkuwa da su, ƙaruwar ƙungiyoyin ýan ta’adda, da rashin ayyukan yi. 

Shugaban Gidauniyar Shirya Musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa, reshen Jihar Filato, wanda kuma Darakta ne a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Filato, Alhaji Ibrahim Kaku ya yi kira ga gwamnatin jihar ta riƙa ɗaukar nauyin jigilar ɗaliban da za su wakilci jihar a Babbar Musabaƙa ta ƙasa. 

A ƙarshen Musabaƙar da aka ware mako guda ana yi, Anas Abubakar daga ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, shi ne ya samu nasarar zama Gwarzon Shekara na bana, kuma zai wakilci Jihar Filato a Babbar Musabaƙa ta ƙasa da za a gudanar a Jihar Kebbi.

By ukarofi