
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim, matar Mai Martaba Sarkin Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, ta rasu bayan fama da wani dogo rashin lafiya.
Sakataren Gwamnatin jihar Neja (SSG), Alhaji Abubakar Usman ya sanar da rasuwarta a wata takarda, ranar Alhamis.
Ya bayyana rashin marigayiyar a matsayin abin baƙin ciki ga Masarautar Suleja da ma jihar Neja baki ɗaya.
Ya kuma yaba mata bisa sadaukarwarta a matsayinta na uwa kuma jigon al’umma wadda hidimarta ta inganta rayukan jama’a da dama.
Haka kuma ya jinjina wa ƙoƙarinta ga fannin ilimi musamman wajen zama shugabar makarantar Rahama School, Suleja, inda ta yi aiki tuƙuru wajen inganta harkar koyon karatu a masarautar.
