Daga JOHN D. WADA a Keffi
Sanata dake wakiltar shiyar Nasarawa ta yamma da ta ƙunshi ƙananan hukumomi biyar wato Karu da Nasarawa da Keffi da Kokona da kuma Toto a jihar Nasarawa, kuma ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC, sanata Aliyu Wadada ya bayar da kyautar wata sabuwar mota ƙirar sharon wa shugaban ƙungiyar nan na masu manyan motocin sufuri da ake kira NATO a turance na ƙaramar hukumar Keffi kuma mataimakin shugaban ƙungiyar ta NATO na jihar baki ɗaya. Har ila yau shine kuma darakta janar na kamfanin Maiwada Sidi motor transport limited sa’anan kuma shugaban ƙungiyar masu tuƙin baburan power-bike na jihar ta Nasarawa wato Hon. Sidi Maiwada.
Da yake jawabi jim kaɗan kafin ya miƙa makullin motar ga hon. Sidi Maiwada, babban daraktan kamfen na sanata Aliyu Wadada a jihar wanda ya wakilci sanatan, Alhaji Bello Ramalan ya taya Sidi Maiwada murnar abin arzikin da ya samu daga gun uban gidan sa inda yace tabbas sanata Aliyu Wadada ya ga ya dace ne ya saka masa da alheri bayan ya yi la’akari da gagaruman gudumawa da shi Maiwada ya daɗe yana bayarwa wajen cigaban harkokin siyasar sa a ƙaramar hukumar ta Keffi da ma jihar baki ɗaya.
Yace tabbas Hon. Sidi Maiwada ya cancanci kyautar don yana ɗaya daga cikin mahimman mutane da sanata Wadada ke matuƙar alfa’ari da su a tafiyar sa ta siyasa zuwa yanzu.
Darakta janar na kamfen na sanatan, Alhaji Bello Ramalan ya ƙara da cewa ya tabbata cewa wannan karamcin sai sake ƙarawa Hon. Sidi Maiwada ƙwarin gwiwa na cigaba da gudanar da kyawawan ayyukan da yake yi don tabbatar da nasarrar sanatan musammam a yanzu da ake shirye-shiryen zaɓukan 2027 dake tafe.
Shima da yake maida martanin jawabi wanda aka bai wa kyautar sabuwar motar, Hon. Sidi Maiwada ya gode wa sanata Wadada game da karamcin inda ya kuma ya yi amfani da damar ya sanar cewa wannan ba shine iya aikin alheri da sanata Wadada yayi masa ba inda yace kafin wannan ma Wadada yayi masa da al’ummarsa wasu ayyukan cigaba da dama da suka haɗa da kafa wasu na’urorin wutar lantarki na solar na zamani da kyautar sabbin babura da bohole-bohole da dai sauran su da dama.
Hon. Sidi Maiwada ya ƙara da cewa karamcin motar ba shakka zai je nesa ba kusa ba wajen inganta harkokin tabbatar da nasarar sanatan a fafatawar kujerar gwamnan jihar da yake nema inda yayi alƙawarin cigaba da yin duka mai yuwa don tabbatar Sanata Wadada ya cimma burin nasa na zama gwamnan gobe a jihar ta Nasarawa a 2027.
Wakilin mu a jihar John D. Wada ya kuma ruwaito cewa sauran abubuwa da aka gudanar a yayin miƙa makullin motar wadda aka gudanar cikin kalilar lokaci sun haɗa da miƙa makullin motar ga shi Hon. Sidi Maiwada da D.G Bello Ramalan yayi da ɗaukar hotuna da sauran su, inda daga bisani kuma Maiwada ya shiga motar ya tuka da kansa a hukumamce.
