Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan ilimi a jihar Katsina Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya faɗawa manema labarai a lokacin da yake bayani kan rufe makarantun firamare da sakandare a jihar.
Ya ce ganin abinda ya faru a jihohin Kebbi, Niger da kwara yasa gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin rufe makarantun domin kaucewa afkuwar lamarin.
Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi gaggawar buɗe makarantun ba amma tana bibiyar abubbuwan da ke faruwa.
Jihar Katsina wanda ta na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da rashin tsaro,kusan itace ta farko da ta shiga cikin wannan yanayi inda a shekarun baya yan bindiga suka sace ɗaliban wasu makarantar sakandare su fiyeda 350.
Yanzu dai kusan duk makarantu na Firamare da Sakandare a faɗin jihar suna rufe.
