
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta samu amincewa da lasisi a hukumance daga Ma’aikatar Lafiyar Saudiyya ga cibiyoyin lafiyarta da aka samar don kula da lafiyar maniyyata ‘yan Nijeriya yayin aikin hajjin 2026.
Wannan ya nuna cewa tawagar lafiya ta NAHCON ta samun damar fara ayyukan kula da maniyyatan a ƙasa mai tsarki.
An samar da waɗannan cibiyoyi ne musamman don samar da magani ga maniyyatan Nijeriya a matakin farko ciki har da neman shawarwari, kulawar matakin farko da magani ga ƙananan cutuka.
Akan haka ne NAHCON ta sanar da maniyyatan cewa wajibi ne su nuna katinsu na Nusuk da fasfo ɗin ƙasa-da-ƙasa domin tantancewa da kuma gabatar da takardar bada magani.
Yayin da aka gano cewa cutar mutum na buƙatar kulawa ta manyan likitoci, sai a tura shi zuwa ga asibitocin da ƙasar ta amince da su, ciki har da Asibitin Sarki Fahad da wasu asibitoci na musamman a Saudi.
Tuni dai NAHCON ta ce, asibitinta na Madinah ya fara aiki sosai tun tsawon kwanaki huɗu da suka gabata wajen ba wa maniyyatan Nijeriya kulawar lafiya daga matsalolinsu.
Cibiyoyin lafiyar sun haɗa da NAHCON clinic, da ke yankin Shara Sittin, Makkah lusa da otal ɗin Humaira, layin Umm Al-Qura kusa da tsohon gidan man Al-Maatani, Makkah.
Sai kuma NAHCON clinic Misfalah na yankin Al-Tadwa, Makkah a otal ɗin Maatouq Al Qarhi, bayan otal ɗin Millennium, layin Ibrahim Khalil, Al-Tadwa, Makkah, da kuma NAHCON clinic na yankin layin Mansour a Niger House No. 1, bayan Muasasat Alnaqd.
