
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, sun yi ram da Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Makamashi ta Ƙasa (ECN), Dakta Mustapha Abdullahi bisa zargin sa da hannu a almundahanar wasu maƙudan kuɗaɗe da jimillar adadinsu ya kai Naira biliyan 500.
A ranar Laraba wata majiya daga EFCC da ta nemi a sakaye sunanta, ta ce an kama Dakta Abdullahi ne a Abuja, wanda a yanzu yana hannun hukumar.
A cewarta, masu bincike suna bincike ne akan zargin hada-hadar kuɗaɗe da suka kai kusan biliyan N500 da aka danganta shi da su.
“Mun kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Ƙasa, Dakta Mustapha Abdullahi bisa laifukan badaƙalar kuɗaɗe,” inji majiyar.
Yunƙurin samun tabbacin al’amarin daga kakakin EFCC, Dele Oyewale bai yi nasara ba saboda ba a same shi ba yayin haɗa wannan rahoton.
A ranar 24 ga watan Oktoban 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya naɗa daktan a matsayin Shugaban ECN.
