Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta tabbatar wa alhazan Nijeriya cewa za ta mayar musu da kuɗin ayyukan da suka biya amma ba su samu ba yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Abba Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin Taron Masu Ruwa da Tsaki kan Bitar Hajjin 2026 da Tsare-tsaren Garambawul na NAHCON, inda ya ce tuni hukumar ta fara tantance asusun kuɗaɗe tare da kamfanonin da suka ba da hidima a Saudiyya.
Ya bayyana cewa, bayan kammala aikin Hajji, NAHCON ta fara amfani da tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyoyin da aka ƙulla da kamfanonin domin tabbatar da an ɗauki alhakin duk wata gazawa da aka samu wajen ba alhazai hidima.
Shugaban NAHCON ya kuma gargaɗi kamfanonin da Nijeriya ke aiki da su a Saudiyya cewa zamanin gazawa wajen cika alƙawuran kwangila ba tare da hukunci ba ya ƙare.
“Dole ne alhazai su samu diyya kan duk wani aikin da aka biya amma aka yi masa gazawa. Daga yanzu, irin aikin da kamfani ya yi ne zai ƙayyade ko za a ci gaba da ba shi aiki,” inji shi.
Jakada Isma’il Abba Yusuf ya ce Hajjin shekarar 1447 Hijira/2026 Miladiyya ta samu nasarori da dama, ciki har da jigilar alhazai cikin tsari, inganta tsarin fitar da biza ta hanyar manhajar Nusuk, bunƙasa ayyukan lafiya, da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin NAHCON, Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin yawon Hajji masu lasisi.
Sai dai ya amince cewa an samu wasu matsaloli, inda ya bayyana cewa alhazai 109 sun kauce wa gwajin lafiya na wajibi kafin tafiya aikin Hajji.
A cewarsa, an kuma samu ƙarancin inganci a wasu fannoni, musamman wajen samar da abinci a yankin Masha’ir, rashin cikakken bin yarjejeniyar da wasu kamfanonin hidima suka yi, matsaloli a ɓangaren masauki da sufuri, da kuma rauni a tsarin sa ido da tabbatar da bin ƙa’idojin da hukumar ke amfani da shi.
Shugaban NAHCON ya ce ba a kira taron ne kawai domin yin bitar Hajjin da aka kammala ba, har ma domin sake fasalin yadda ake gudanar da harkokin Hajji a Nijeriya domin inganta hidima ga alhazai.
Ya bayyana cewa sabon tsarin garambawul na hukumar zai mayar da hankali kan fara shirye-shiryen Hajji tun da wuri, ƙirƙirar manhajar dijital guda ɗaya ta ƙasa domin rajistar Hajji da Umara, da kuma ƙarfafa gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen Hajji.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, wanda tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr. Aliyu Modibbo Umar, ya wakilta, ya ce gudanar da harkokin Hajji na buƙatar cikakkiyar gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai.
Ya tunatar da jami’an Hajji cewa kula da alhazai ba aikin gwamnati kawai ba ne, nauyi ne na addini da ke tattare da babban lada, domin Musulmi sun yi imani cewa ladan Hajjin da Allah Ya karɓa shi ne Aljanna.
“Ku tuna cewa duk wanda yake gudanar da harkokin Hajji yana da babban nauyi. ƙafarsa ɗaya tana hanyar Aljanna, amma ɗayar na iya karkata idan bai yi abin da ya dace ba,” inji shi.
