Daga MUKHTAR YAKUBU
Tun bayan fitar labarin damfarar da wani mai suna Bashir ya yi wa Jaruma Halisa Muhammad kan tafiyar ta zuwa ƙasar Saudi Arabia neman magani a kwanakin baya, jama’a suka zuba ido su ga irin matakin da hukumomi da sauran al’umma za su bi domin kwato wa wannan marar lafiya Halisa Muhammad da take cikin mawuyacin hali domin a ceto rayuwarta.
Wannan hali da baiwar Allah Halisa Muhammad ta shiga ya taɓa ziciyar mutane, saboda tsawon lokaci da ta shafe cikin rashin lafiya da kuma neman taimakon yadda za ta ceto rayuwarta. A daidai lokacin da damar ta samu na tafiyar neman lafiyar kuma ta haɗu da wata jarrabawa ta damfarar ta da aka yi.
A yanzu da yake an ɗauki lokaci, don haka muka nemi jin ta bakin Jaruma Halisa Muhammad don jin yadda aka kwana. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: A kwanakin baya kin shirya tafiya zuwa ƙasar Saudi Arabia don neman lafiyar cutar kansar mama da kike fama da ita, sai kuma aka samu wani ya damfare ki kuɗin tafiyar, don haka za mu so ki yi mana bayanin yadda al’amarin ma ya faru.
JARUMA HALISA: To assalamu alaikum. Sunana Halisa Muhammad wadda nake fama da ciwon kansar mama wadda mutane da dama musamman ‘yan Kannywood suka fara ɗaukar nauyin ciwon suka yi iya gwargwadon iyawar su, saboda ciwo ne mai wahalar sha’ani, wanda har aka zo ga taimakon mutanen da ba ‘yan fim ba suka bani gudunmawar su sosai iya gwargwadon iyawar su. Kuma har aka zo aka saka a soshiyal midiya wanda Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗauki nauyin alluraina kuma ya ba mu kuɗi Naira miliyan 15 domin mu sayi allurai da magani.
To sai wani bawan Allah mai suna Bashir Abdullahi wanda ya yi kiran kansa mai yin hanya zuwa tafiye-tafiye ya ce mana ya zo da taimako akwai wani asibiti a ƙasar Saudi Arabia a Madina, da ya kai mahaifiyarsa, don haka zai taimaka ya kaini mu karasa waɗannan magunguna, kawai dai abin da yake buƙata a wajen mu kuɗaɗen bisa da na tikiti. To daga nan muka fara wannan mu’amala da shi tun cikin azumi har aka zo tafiya aikin Hajji kullum yana faɗar magana daban. Yau ya ce a ba shi dubu 500,000 gobe ya ce miliyan ɗaya, har ya kai ya karɓi miliyan bakwai da ɗari bayar.
Daga nan ya saka mana ranar tafiya ya aiko mana bisa da tikiti, muka je filin jirgi don tafiya, to sai aka ce mun makara wajen tafiya. Don haka muka kira shi muka faɗa masa, har ya rinƙa faɗa a kan abin da aka yi mana.
To a haka dai yana canza tikiti sai da muka sai da muka je filin jirgi sau bakwai zuwa takwas, don akwai ranar da muka je sau uku ma. Amma dai da muka ga abin ya ci tura sai muka tambayi mahukuntan filin jirgin kan ya abin yake ciki?
Shi manajan tafiye tafiye na wajen da muka same shi muka sanar da shi halin da muke ciki. Sai ya buɗe kwamfiyuta ya duba tikitin mu nan ya tabbatar mana ai ba a saye shi ba ma a hukumance don ba a tama ma sayen sa ba kamar dai yadda kwamciyuta ta nuna.
To daga nan sai muka ce ga bisa ita ma a gwada man, ita ma da aka saka a kwamfiyuta ta ki ɗauka, sai daga nan ne muka gane mun faɗa hannun dan damfara ne ya damfare mu ya ba mu tikiti da bisa na bogi.
To sai muka dawo muka same shi muka sanar da shi kuma ya amsa haka ne, amma mu jira shi zai biya mu kuɗinmu.
To shiru shiru sati ɗaya kwana goma, saboda sakamakon ciwo ya dawo baya za mu koma asibiti mu ci gaba da magani, sai muka je muka samu iyayensa muka sanar da su, suka ce za su taimaka za su yi masa magana. Amma duk aka yi abu bai yi ba.
Sai muka koma muka kai kara Bompai wajen Hukumar ‘Yan sanda sannan muka je DSS nan ma dai abin ya ci tura, har na ƙara zuwa na yi rubutu a doshiyal midiya duk dai shiru.
Sai na yi sa’a ta hanyar soshiyal midiya na samu wani babban lauya, Barista Dantani ya shigo ya ɗauke ni muka je DSS muka shigar da ƙara. Kuma a ranar ma har an je gidansa domin a kama shi babu shi babu dalilin sa. To har yanzu a wannan maganar muke
Abih dai da na sani an samu na ci gaba, bisa wannan ƙoƙari da shi Barista Dantani yake yi ya turo dubu ɗari bayar, ya ce ai zai bayar. Daga baya ya kuma bada wata ɗari bayar din. To aka ci gaba da bibiyar sa dai ya ƙara bayar da miliyan ɗaya, a yanzu abin da ya bayar miliyan biyu kenan, saura miliyan biyar da ɗari bayar. Kuma yanzu dai babu amo ba labari.
Su a ta ɓangaren hukumomi wanne matakai suke ci gaba da ɗauka na ganin ya dawo da kuɗin ko an kai ga kama shi?
To har yanzu dai ana ta ƙoƙari na a kama shi ko kuma ya zo ya kawo kansa ne. Ana samun sa a waya, amma idan an je wajen da yake ba a samun sa.
To ita maganar har yanzu ba ta kai ga kotu ba kenan?
A’a ba ta kai ga kotu ba, saboda ai ba a same shi ba da har za a kai shi kotun.
A yanzu da ake cikin wannan yanayin wanne hali kike ciki dangane da jikinki?
E to da yake ita kansa matakai ne guda biyar zuwa shida. To Alhamdulillah, mun yi huɗu saura guda biyu wanda shi ne abin da ya rage a yanzu. Kuma waɗannan kuɗaɗen su ne za mu yi amfani da su wajen sayen magunguna da ake ɗora mutum a kansu kusan shekaru biyar wasu shekara huɗu, idan an yi gwaje-gwaje.
To shi gwajin da za mu je, ba a yin sa a nan Kano ko Abuja a Legas ake yin sa, kuma idan za ka tafi ana neman a kalla ka riƙe miliyan huɗu, sannan idan an yi ka kawo sakamakon gwajin, daga nan sai kuma a ɗora ka a kan magunguna. Wannan shi ne abin da ya rage mini kuma na samu kaina a wannan jarrabawa ta damfara.
Kenan dai har yanzu Halisa Muhammad tana neman addu’a da taimakon mutanen kan halin da kike ciki?
Gaskiya ne halin da nake ciki kenan na neman taimakon domin na samu tafiya wannan gwaje-gwajen, ko dai a taimaka mini wajen kwato mini hakkina a wajen wannan bawan Allah ko kuma a samu waɗanda za su taimaka mini da kuɗin da zan ci gaba da kula da lafiya ta.
A can baya an yi aiki da gwaje gwaje. Shin ya lalace ne ko wata matsala aka samu?
Ai daman matakan guda shida ne kamar yadda na faɗa maka. To mun yi guda huɗu, tun da farko an kwanta a asibiti an yi kemo, kuma aka zo aka yi tiyata, sannan aka ƙara yin kemo. Aka zo kuma aka yi gwaje-gwaje kuma aka fara allurar, wadda ita allurar muka yi kashi shida wanda a lokacin hankali ya tashi saboda allura ta yanke ba mu da kuɗin ta ba mu da dalili. Sai aka zo mai girma Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf shi ne ya bayar da kuɗin allurar muka saye su gaba ɗaya. To da muka gama sai kuma wannan gwaje-gwaje, wanda idan ƙasashen da suka ci gaba ne, to gwajin zai zama kyauta ake yi. To musamman ƙasar Saudi Arabia za ka je ka yi ziyara ka yi addu’a ka yi gwajin, kuma ka dawo gida da gwajin a ɗora ka a kan magani. Ka ji yadda tsarin yake.
Ko wanne kira za ki yi ga al’umma dangane da halin da kike ciki?
To kira da zan yi ga al’umma a matsayina ta shugabar ƙungiyar wayar da kai a kan ciwon kansar mama shi ne, mata da maza su kula da lafiyarsu, musamman wannan rashin lafiyar ta cutar kansar mama, domin ciwo ne da yake yaɗuwa kamar wutar daji. Sannan gwamnatocin mu idan mun fito neman taimako ga masu wannan ciwon, don Allah a taimaka mana. Ina yi wa kowa fatan alheri.
Madalla mun gode.
To ni ma na gode sosai.
