Magance matsalar tsaro

Spread the love

Mu na ƙara ba gwamnatoci shawara dangane da samun tubka da warwara ta fuskar magance matsalar tsaro. Tabbas wasu rahotanni da daɗin ji domin ana samun nasarori kamar hallaka jagororin Boko Haram, Abubakar shekau, da miƙa wuyan wasu dubban mabiyansa. Haka rahoton hallaka jagoran ISWAP Albarnawi da kuma wanda aka naɗa magajinsa, baya ga hallaka mutane kamar Buharin Daji da Awwalun Daudawa duka nasara ce. Abun mamaki daban tsoro yadda a makon ƙarshe na wancen wata Oktoba aka samu gano wata maƙera ta bindiga ƙirar AK-47 a Jos da ke Jihar Filato, haka a wata arangama jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun wargaza wata maboyar ’yan ta’adda tare da kama wani boka da wasu kayan aikinshi da makamai a rahoton BBC hausa. Hakan ke fiddo ƙoƙarin gwamnatoci wajen yaƙar ta’addanci amma da sauran aiki. Magance fatara da talauci tare da fallasa ma su ɗaukar nauyin ta’adda ita ce hanya mai kyau. A ƙara baza koma a ko ina.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519\08080140820.

By ukarofi