Hana motoci daga Arewa shiga Legas ba daidai ba ne – RTEAN

….Ta buƙaci Gwamnatin jihar ta gaggauta janye matakin hanin

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa (RTEAN) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta janye matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar.

Cikin sanarwar manema labaraida ya fitar ranar Alhamis, Babban Sakataren RTEAN, Kwamred Yusuf Ibrahim Adeniyi, ya ce ƙungiyar ta samu labari daga reshenta na Jihar Kwara da wasu jihohin Arewa cewa Gwamnatin Legas ta ɗauki matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar.

Ya ce, “Umarnin hakan ya fito ne daga jami’in Gwamnatin Jihar, Seyi Bamigbose wanda shi ne Mataimakin Shugaba na kwamitin kula da tashoshin mota wanda Gwamnatin Jihar ta kafa bayan dakatar da RTEAN reshen Legas daga ayyukanta.

“Batun da an riga da an ɗauke shi zuwa gaban Kotun Masana’antu ta Ƙasa (NIC) inda kotun ta ba da odar ɓangarorin da lamarin ya shafa a zauna da juna lafiya kowa ya ci gaba da aikinsa.

“Amma sai Gwamnatin Legas ta ƙi tanƙwara kwamitin kula da tashoshin kan bin umarmin kotun,” in ji Adeniyi.

Ya ƙara da cewa, yanzu RTEAN ta soma yarda cewa take-taken Gwamnatin Legas shi ne saɓa wa umarnin da kotu ta bayar.

Ya ce matakin hana motocin fasinja daga Arewa gudanar da harkokinsu a jihar, mataki ne da ka iya haifar da tashin-tashina a tsakanin al’umma.

Don haka ya ce RTEAN na kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta janye wannan mataki da ta ɗauka don bai wa kowa ‘yancin yin zirga-zirg kamar yadda Sashe na 41 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tabbatar.

Yana mai cewa, RTEAN ƙungiya ce wadda dokar ƙasa ta san da zamanta, kuma mai gudanar da harkokinta daidai da doka.