Rawar da Ma’aikatar Jinƙai ta taka a yaƙi da rashin tsaro, cin zarafin yara da gurɓata muhalli

PAUL OKAH ya rawaito cewa, Ma’aikatar Jinƙai da Kawar da Annoba da Gina Al’umma  (FMHADMSD) ta kasance a sahun gaba wajen yaqar rashin tsaro a Nijeriya. Hukumar kuma ta a ƙoƙarin ganin bayan ɗaukar yara ‘yan ƙasa da shekaru 18 don gabatar da  ayyukan ta’addanci da ƙaddamar da kwamiti a kan kwashe gutsattsarin abubuwan fashewa da suka gurɓata muhalli suke illatar da al’umma.

Akwai wani azanci da yake cewa, harkar tsaro nauyi ne a kan kowa da kowa, saboda haka, Ma’aikatar ta haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a sassa daban-daban na ƙasar nan. 

Ma’aikatar jinƙai ta Tarayya (FMHADMSD), wacce Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita a shekarar 2019, an ɗaura mata nauyin tsarawa da tabbatar da tsaron al’umma da kuma ba da jin ƙai a ƙasar idan buƙatar hakan ta taso.  

Masu ruwa da tsaki sun shawarta a kan yadda za a ɓullo wa lamarin ɗaukar yara ƙasa da shekaru 18 a harkar aikin ta’addanci.

A ranar 10 ga watan Janairu ne babban sakataren na Ma’aikatar jin qai, Dakta Nasiru Sani-Gwarzo, ya bayyana yadda yara ‘yan ƙasa da 18 suke shiga ƙungiyoyi na ta’addanci l, abinda ya ce hakan yana kawo rashin tsaro a jihohi daban-daban na ƙasar. Wanda hakan barazana zai iya zama ga gwamnatin Tarayya.  

Dakta Gwarzo a yayin da yake jawabin nan a Abuja a yayin wani taro na wayar da kai ya bayyana takaicinsa a kan yadda ake amfani da yara ‘yan qasa da shekaru 18 wajen ayyukan ta’addanci. A cewar sa, abin zai iya zama babbar barazana a kan tsaron ƙasar nan.

Domin a cewar sa, wancan rukunin matasan su suka fi saurin lanƙwasuwa, vatarwa, da hilata don shiga ƙungiyoyi na tsaurin aƙida. Kuma acewarsa abin yana ya ƙara yaɗuwa. 

Wannan dalili ne a cewar sa ya sa gwamnati ta ɗauki ɓangaren ceto waɗancan matasa da marayu, abinda ya tilasta Ma’aikatar ta jin ƙai ta shirya wani shiri na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a don samo bakin zaren wannan matsala.

Gwamnati ta yi ƙoƙarin gano dabarun da waɗancan ɓata-gari suke amfani da su wajen shigar da matasan ‘yan ƙasa da 18 su mayar da su ‘yan sara-suka. Kuma haka, gwamnatin za ta ɗauki matakan daƙile hakan.

Masu ruwa da tsaki za su samar da matakai da dabarun da za a dinga nazarin matasan ‘yan ƙasa da 18 da irin ɗabi’un da suke yi har a gano halin da suka faɗa. Waɗanda ba su faɗa ba kuma, za a yi ƙoƙarin ilmantar da su a kan yadda ake amfani da matasa wajen aikata ayyukan ɓarna da illar hakan gare su. 

Shi ma a nasa bayanin, ƙwararre a kan harkar kwantar da tashin hankali sakamakon tsattsauran ra’ayi, Daraktan Zartarwa na  Renvoi Consult, Mista Saka Azimazi, ya bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta fara magance matsalar da take kawowa har iyaye su dinga watsar da yaransu, matuƙar dai gwamnatin da gaske take yi tana son daƙile matsalar shigar matasa ta’addancin. 

Haka zalika, Shugabar tsare-tsare na ƙasa matashiyar jakadiya Barista Zainab Khaleel, ta bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta daƙile tsarin rayuwar al’umma wanda ya ba wa yara ikon zartar da hukunci a kan al’amuran da suka shafe su.

Horas da ma’aikata a kan harkar tsaron-kai:

A ranar 15 ga Nuwamban shekarar da ta gabata ne dai ma’aikatar ta shirya bitar horas da ma’aikatanta a kan yadda za su kare kansu daga masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a Abuja.  

Shugabar sashen ayyuka na musamman  Malama Nadia Soso Muhammed, wacce mataimakiyarta Malama Dinatu Wuyah, ta wakilta ta bayyana cewa, horaswar ta zama dole ne saboda ayyukan da ma’aikatar take gudanarwa a ɓangarori daban-daban na ƙasar, inda ma’aikatanta za su iya cin karo da tsautsayi kamar na masu garkuwa da mutane.

Domin a cewar ta, yanzu Nijeriya ta kasance koyaushe a cikin samun rahotannin garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda da ɓata-garin daji suke yi.  A cewar ta, rashin tsaron ya kawo koma-baya a harkar tattalin arziki, cigaban ƙasa, harkar siyasa, da kuma tsaro da zaman lafiya a ƙasar. Sannan kuma ya tarwatsa mutane da dama daga matsugunnansu. 

Wannan ya sa ma’aikatar take ƙoƙarin ganin ta yi aiki ba ji, ba gani don kare al’umma daga wannan matsala ta rashin tsaro. A don haka a cewar ta, wannan horaswa ta zama dole ga ma’aikatan da za su yi wa Ma’aikatar wannan aiki. A kan haka ta ce tana fata ma’aikatan su zama masu wa’azi wajen ɗaukar wannan darasin domin su ci moriyar samun hanyoyin kare kansu yayin gudanar da ayyukansu. 

Ɗaya daga cikin darussan da aka koyar a wannan bita dai shi ne, a kan garkuwa da mutane, da yadda za a yi cinikin diyya da yadda za a biya wanda Kwamanda Musa Salmanu (mai ritaya), ya gabatar. 

A jawabinsa na rufewa, mataimakin a musamman ga shugaba Muhammadu Buhari a kan al’amuran jin-ƙai,  Musa Bungudu, ya yaba wa ma’aikatar a kan wannan horaswa da ta gudanar ga ma’aikatanta sannan ya ba ta shawara a kan a ƙara faɗaɗa wannan bita yadda ƙananan ma’aikatanta za su samu, da kuma ma’aikatan hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), da sauran masu ruwa da tsaki.  

Haka ya roƙe su da a ƙara yawan kwanakin bitar ya zama sama da kwana ɗaya domin muhimmancinsa. Sannan ya ja kunnen mahalartan a kan su guji nuna tsadaddun motoci ko tufafi a bainar jama’a. Hakan zai iya jawo hankalin masu garkuwa i zuwa gare su. 

Minista ta ƙaddamar da kwamitin ceto al’umma daga illar gutsattsarin abubuwan fashewa:

Ta hanyar yin biyayya ga umarnin Shugaban ƙasa  Muhammadu Buhari, Ma’aikatar jin ƙai, ta zo da mafita don magance illolin gutsattsarin abubuwan fashewa. Ministar  Ma’aikatar, Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da kwamiti a ranar 20 ga watan Oktoba (mai suna MAC) don ceto al’ummar yankin Arewa maso gabashin ƙasar nan daga cutarwar gurɓatar yanayin abubuwan fashewa.  

A yayin da take jawabi a wajen ƙaddamarwar, ministar ta bayyana cewa, a duk sanda aka ƙare bata-kashi na makamai, filin dagar  zai kasance ya gurɓata da gutsattsarin abubuwan fashewa, waɗanda wasu daga cikinsu za su iya kasancewa masu haɗarin gaske.

Wasu kuma alburusai ne, da Ababen fashewa, waɗanda aka harba, amma ba su tashi ba. Kamar yadda muke iya gani a wasu sassan na Duniya, sai a manta ma an kammala yaƙin, amma waɗannan gutsattsarin na alburusai da Ababen fashewa, sukan cigaba da kashewa, naƙastawa, gami da cutar da mutane a yayin gudanar da al’amuransu na yau da kullum. Sannan kuma suna da illa ga Ababen more rayuwa na al’umma.

A nan a Nijeriya kuma, a yayin da zaman lafiya da tsaro suke ƙara bunƙasa a yankin Arewa maso gabashin ƙasar, sai dai kuma wasu da basu ji ba, ba su gani ba, sun rasa rayukansu, ko hannaye da ƙafafunsa su a sakamakon yin ta’ammali da gutsattsarin Ababen fashewar. 

A cewar rahoton Shirin jin ƙai na Majalisar ɗinkin Duniya na zagayen shejarar 2022 wanda aka gabatar a watan Fabrairu na shekarar, ƙiyasin mutane miliyan 1.2 a jihohin Borno, Adamawa da Yobe suke cigaba da shafuwa da illar gutsattsarin abubuwan fashewa. Kama daga  mazauna garin, ‘yan gudun hijira, sansanin ‘yan gudun hijira, har ma da waɗanda suka dawo. 

Ga mazauna yankunan da aka taɓa yaƙi ko bata-kashi na makamai a Arewa maso gabashin ƙasar nan, akan samu dawwamammiyar barazana ta gurvatar muhalli ga mazauna yankin. Haka gutsattsarin waɗannan makamai sukan iya hana sake yin gine-gine kuma sukan shafi al’amuran tattalin arziki.

Gidaje da makarantu da asinmbitoci ma ba za su ginu ba a irin waɗannan wurare ba, har sai an gyara shi. Sannan ba damar a yi shuka a wannan gurvataccen muhalli. 

Daga shekarar 2016 zuwa yau, aƙalla mutane 755 suka rasa rayukansu, kuma a ƙalla guda 1,321 suka jikkata a sakamakon gurɓatar muhalli da gutsattsarin Ababen fashewar. Kuma wannan alƙalumman za su iya kasancewa ma sun zarce hakan. Mafi yawansu maza ne waɗanda suke ƙoƙarin noma ko tafiye-tafiye ko tsintar ƙarafuna na jari-bola. Kodayake, mata da yara ƙanana ma suna iya haɗuwa da barazanar hakan ta hanyar nemo itace, ko kiwo ko kuma yara idan suna wasa. 

Duk da haka kuma, rahotanni sun bayyana cewa, adadin fashewar Ababen fashewar ya qaru a shekarar 2021.Inda aka samu jimillar Ababen fashewa  293 kamar yadda aka samu 295 a shekarar 2020.

A sakamakon wannan dalili ne shugaba  Muhammadu Buhari, ya ba da umarni ga Ma’aikatar jin ƙai ta Tarayya da ta lalubo bakin zaren da zai kawo mafita ga barazanar Ababen fashewar ga al’umma. 

Wannan umarni na shugaban ƙasa na neman a ceto al’ummar Arewa maso gabashin Nijeriya ya sanya ma’aikatar jin ƙai ta ƙaddamar da shirin kwamitin ‘Mine Action’ (MAC). Wanda shi ne ake sa ran ya kawo mafita ga gurɓatar muhallin da ya samu sakamakon gutsattsarin makaman.